Masarautar Zazzau ta yi sabbin naɗe-naɗe

Daga WAKILINMU

Masarautar Zazzau ta naɗa ƙarin sabbin hakimai takwas tare da miƙa musu takardun fara aiki.

Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ne ya ƙaddamar da sabbin hakiman a wani ƙwarya-ƙwaryan biki a fadarsa da ke birnin Zariya.

An naɗa su ne bayan amincewar Gwmanan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ta hannun Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Masarautu ta jihar.

Sanarwar da jami’in yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na masarautar, Abdullahi Aliyu Kwarbai, ya fitar ta nuna waɗanda naɗin ya shafa sun haɗa da:

Alhaji Sufiyanu Umar Usman, Ƙarfen Dawakin Zazzau a matsayin Hakimin Pambegua, Mohammed Dahiru Dikko, Barde Kankanan Zazzau, a matsayin Hakimin Pala, da kuma Arch. Haruna Abubakar Bamalli, Barde Kerrariyyan Zazzau a matsayin Hakimin Zangon Aya.

Sai kuma Alhaji Kabiru Zubairu Madaucin Arewan Zazzau – Hakimin Barnawa, Dr. Bello Lawal Durumin Zazzau, – Hakimin Gubuchi.

Alhaji Abdulkarim Zailani da Alhaji Auwalu Aliyu Damau da Alhaji Aminu Mohammed Ashiru a matsayin hakiman Sabon Birni, Damau da kuma Hunkuyi.

Baki ɗayansu, Sarkin Zazzau ya miƙa musu takardar fara aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *