Masari ya buƙaci ‘yan Nijeriya su ƙara haƙuri da gwamnatin APC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Masari, ya buƙaci ‘yan Nijeriya su nuna ƙarin haƙuri da gwamnatin Jam’iyyar All Progressiɓes Congress (APC), yana mai cewa matsalolin tattalin arzikin da ake fuskanta na daga cikin al’amuran duniya ne kuma ba na musamman a Nijeriya ba.

Masari ya bayyana wannan jawabi ne a ranar Lahadi a ƙafur, ƙaramar Hukumar ƙafur, a lokacin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen ƙananan hukumomi da za a gudanar ranar 15 ga Fabrairu.

Ya yi magana ne game da rahotanni da suka bayyana a shafukan sada zumunta cewa wasu ‘yan siyasa suna haɗa kai domin kafa sabuwar haɗin gwiwa, wanda ya bayyana a matsayin wani yunƙuri na waɗanda suka rasa goyon bayan siyasa a cikin APC, musamman wajen samun muƙamai da tallafi.

Masari ya jaddada cewa irin waɗannan yunƙurin ba za su hana APC ci gaba da ƙirƙira da aiwatar da shirye-shiryen da za su taimaka wajen sauƙaƙe wahalhalun da talakawa ke fuskanta ba. Ya kuma tabbatar da jajircewarsa ga ƙa’idojin APC, yana mai cewa, “Ni a APC ne yau, gobe, da koyaushe saboda ba na cikin jam’iyyar don neman muƙamin siyasa ko wani albashi.”

Tsohon Kakakin Majalisar Tarayyar ya buƙaci mambobin APC da su yada kyawawan ayyukan da ɗabi’un jam’iyyar, yayin da ya roƙi al’umma su ɗauki kowane gazawa a matsayin kuskuren ɗan adam.

Masari ya kuma yi kira ga mutanen ƙaramar Hukumar ƙafur da su fito da yawa domin goyon bayan APC a zaɓen ƙananan hukumomi mai zuwa.