Masari ya janye dokar hana hawa babura a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya janye dokar nan ta hana hawa babura a faɗin jihar.

Bayanin haka yana ƙunshe cikin wata sanarwa da mai ba wa gwamnan jihar shawara kan harkar tsaro, Ibrahim Ahmad Katsina ya fitar.

Gwamna Masari ya bayyana cewar, an janye dokar ne domin ba wa masu bukukuwan Mauludi damar gudanar da hidindinmunsu a sassan jihar.

Watan Rabi’ul Awwal shi ne watan da aka haifi fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W) inda al’umar jihar kan shirya majalisi na karatuttuka don nuna farin cikinsu da samuwar Annnabi S.A.W.

Janye dokar ya fara aiki ne tun daga ranar 14 ga watan Oktoba, sai dai da zarar watan ya ƙare, wato zuwa 20 ga watan Nuwamba, 2022 dokar za ta ci gaba.

Sanarwar wadda Manhaja ta gani ta kuma buƙaci al’umar jihar da su kasance masu bin doka da oda gami da ba wa jami’an tsaro haɗin kai wajen ganin an yaƙi ta’addanci a jihar.

Idan za a iya tunawa, gwamnatin jihar ta kafa dokar hana hawa babura daga ƙarfe 10 na dare zuwa ƙarfe 6 na safe a matsayin wani mataki na daƙile aikace-aikacen ‘yan bindiga waɗanda ke amfani da babura a duk lokacin da za su kai hare-haren ta’addanci.