Mashaya za su ɗanɗana kuɗarsu a Nijeriya sakamakon tashin farashin sinadarin giya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Masu shan barasa a Nijeriya za su fuskanci matsanancin ƙarin kuɗi, kamar yadda Kamfanin Breweries na Nijeriya (NB PLC) ya sanar da ƙarin farashin kayayyakin sa daga ranar 10 ga Agusta, 2023.

Kamfanin NB PLC ya yanke hukuncin ne a wata wasiƙa mai kwanan wata 1 ga Agusta 2023.

Kamfanin ya ba da misali da buƙatar sake duba farashin saboda cigaba da hauhawar farashin kayayyaki da kuma wajibcin rage tasirinsa.

“Muna sanar da ku cewa za mu sake nazarin farashin barasa daga ranar Alhamis 10 ga Agusta 2023.”

Yayin da hauhawar farashin kaya ya kai kashi 22.79 cikin 100 a cikin watan Yuni da kuma yadda ake gudanar da kasuwannin hada-hadar kuɗi da ya kai Naira 869 a dala ɗaya a makon jiya, kamfanoni irin su NB PLC sun fuskanci ƙalubale sosai.

A sakamakon kuɗaɗen da suka samu na rabin shekara, NB PLC ta ba da rahoton asarar Naira biliyan 70.6 a cikin kuɗin da aka samu a cikin 30 ga Yuni, 2023.

Haɗe da hauhawar farashin kayayyaki da hauhawar farashin kayan masarufi, wannan ya haifar da ƙalubale na yanayin kuɗi wajen tafiyar da abubuwa.

Tavarcarewar tattalin arzikin Nijeriya gaba ɗaya da kuma faɗuwar darajar kuɗin ƙasar ya ƙara yin tasiri ga samun riba a masana’antu daban-daban, ciki har da sana’o’i.

Tare da an saita qarin farashin da zai fara aiki a ranar 10 ga Agusta, 2023, babu makawa zai yi tasiri a lokacin sayen abubuwa daban-daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *