Daga UMAR GARBA a Katsina
Wani matashi mai suna Ibrahim Mohammed, ya rasa ransa a hannun wasu ‘yan daba da suka yi yunƙurin ƙwace masa wayar salula.
Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Talata a hanyar unguwar Kasuwan Mata, cikin ƙaramar hukumar Funtua ta Jihar Katsina.
Marigayin, wanda aka fi sani da Elale, an ce ya fito ne domin yin sallah a wani masallaci da ke kusa da gidansa a lokacin da wasu da ake zargin ‘yan daba ne suka tare shi tare da yi masa barazana da makami.
Da fari Mohammed yaƙi bayar da wayar tasa ga ɓarayin wayar lamarin da ya kai ga sun zare wuƙa suka kuma daɓa masa ita.
“Sun buƙaci ya miƙa musu wayarsa, inda suka yi masa barazana da wuƙa, amma ya ƙi, inda daga bisani ya yi artabu da su,” in ji wata majiya a yankin.
Lamarin dai ya jefa al’ummar yankin da marigayin ke zaune cikin razani da tashin hankali, inda aka bar ‘yan uwa da iyalansa da alhinin mutuwarsa.
Zuwa haɗa wannan rahoto kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abubakar Aliyu, bai yi wani ƙarin haske ba game da lamarin.
Tuni aka yi jana’izar Mohammed da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar ranar Talata kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, a yayin da masu ta’azziya gami da nuna alhini ke ci gaba da tururuwa zuwa gidansa domin jajanta wa iyalansa.