Masu ƙwacen waya sun tsallake rijiya da baya a Kano

Daga RABI’U SANUSI a Kano

A ci gaba da fafutukar ganin cewa jami’an tsaro sun samu nasarar kawo ƙarshen masu ƙwacen waya a Jihar Kano da ma wasu maƙwabtan jihar, kawo yanzu al’ummar jihar sun fara ɗaukar matakin kare kansu daga ta’addancin ‘yan fashin wayar inda a wasu lokutan sukan yi kisa da jikkata mutane.

A ranar Asabar da misalin ƙarfe 10:30 na dare, wasu ‘yan ƙwacen wayar suka yi ta’asa a kan titin Kabuga.

Lamarin da ya sanya al’umma yin ƙoƙarin kama su a cikin babur din adai-daita sahu amma suka tsere.

Bayanai sun ce jama’a sun samu damar kama babur ɗin inda suka banka masa wuta nan take.

Idan dai za a iya tunawa, Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Kano ta sha alwashin ganin bayan masu ƙwacen waya a Kano da kewaye domin ƙarfafa zaman lafiya a cikin al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *