Masu barazanar hana zaɓe a Nijeriya cika baki kawai su ke yi – Buratai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Babban hafsan sojin qasa na Nijeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Burutai, ya bayyana ƙwarin gwiwa game da zaɓen Nijeriya da za a fara a cikin watan Fabrairun 2023.

Janar Buratai, wanda ɗan kwamitin yaƙin neman zaɓen Cif Bola Ahmed Tinubu, ne na APC a zaɓen, yayin wata ziyara a sashen Hausa na BBC, ya ce yawancin masu barazanar hana zaɓe, magana ce kawai ta fatar baki, ba da gaske suke yi ba.

Ya ce, ‘’Ni a ganina barazana kawai suke, domin sojojin Nijeriya da ‘yan sanda da ma sauran jami’an tsaro sun ɗaura ɗamarar tunkarar duk wanda zai tayar da wani hargitsi a lokacin zaɓe.”

Laftanar Janar Tukur Yusuf Burutai, ya ce akwai fargaba da koke-koken da ake, a kan cewa za a iya samun matsala a lokacin zaɓen mai zuwa, to ya kamata mutane su duba su gani a yanzu akwai ci gaba wajen tabbatar da tsaro a Nijeriya, bisa la’akari da shekarun baya da aka yi zaɓe.

”To idan har a baya a lokacin da ake fama da matsalar taɓarɓarewar tsaro an yi zaɓe lami lafiya, ina ga yanzu an samu ci gaba sosai wajen tabbatar da tsaro, don haka kowa ya kwantar da hankalinsa za a iya zaɓe mai zuwa cikin lumana da kwanciyar hankali, domin jami’an tsaro sun shirya,” inji shi.

Tsohon Babban hafsan sojin ƙasa na Nijeriyar, ya ce a yanzu akwai abubuwa biyu da ya kamata a yi kafin lokacin zaɓen:

‘’Na ɗaya shi ne jami’an tsaro da kuma gwamnati su fito su bayar da tabbaci a kan cewa za a ɗauki matakan da suka dace daidai gwargwado, don ganin cewa an tabbatar da tsaro a lokacin zaɓe, inji shi.

Laftanar Janar Tukur Yusuf Burutai, ya yi wannan jawabin ne a yayin da ya rage makonni a gudanar da babban zaɓe a Nijeriya, kuma zaɓen ya zo ne a dai dai lokacin da ake fuskantar matsaloli da dama a ƙasar, da suka shafi tattalin arziki da kuma tsaro.

Hare-haren da ‘yan bindiga ke kaiwa kan ofisoshin zave musamman a jihohin Kudu maso Gabas, na daga cikin abubuwan da ake ganin za su iya kawo tarnaƙi a zaɓen da ke tafe.

To sai dai kuma duk da fargabar da ake nunawar, Shugaban Ƙasar Muhammadu Buhari, ya jadadda cewa zaɓukan za su gudana kamar yadda aka tsara.

Sannan ita ma hukumar zaɓe ta yi watsi da raɗe-raɗin da wasu bayanai da aka rinƙa yaɗawa kan yiwuwar ɗage zaɓen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *