Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Masu buƙata ta musamman a jihar Ekiti da ke Kudancin Nijeriya sun yi barazanar kai hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC gaban kuliya, kan ƙorafin ƙin tanadar abubuwan da suke buƙata domin shiga zaɓen gwamna da za a yi a jihar ranar 18 ga watan Yuni.
Jaridar Premium Times ta ambato shugaban ƙungiyar masu buƙata ta musamman reshen jihar Ekiti, David Anyaele yana shaida wa ‘yan jarida cewa matuƙar INEC ba ta yi abin da ya dace ba, za su shigar da ƙara kotu kan take haƙƙinsu, da dokokin Nijeriya suka ba su a matsayin ‘yan ƙasa.
Mista Anyaele ya ƙara da cewa “duk wani yunƙuri na hana ‘ya’yan ƙungiyarmu kaɗa ƙuri’a zai sa mu ƙalubalanci INEC a gaban kuliya domin take dokar da Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaɓa wa hannu kan walwalarmu.”
Ya ƙara da cewa ƙungiyarsu ta damu matuƙa kan halin taɓarɓarewar tsaron da ake fuskanta, musamman yadda ‘yan daba ke hana wasu kaɗa ƙuri’a. Don haka ya buƙaci hukumar zaɓen ta yi aikin haɗin gwiwa da ‘yan sanda domin ba su tsaron da ya dace a lokacin zaɓe.