Masu garkuwa da mutane sun shata daga a junan su: Sama da mutum ɗari sun mutu

Daga FATUHU MUSTAPHA

A ranar Alhamis da misalin ƙarfe 5 na yamma ne wani gungun masu garkuwa da mutane suka nemi kutsa kai cikin garin Illela na Ƙaramar Hukumar Safana da ke Jihar Katsina. Wannan kutse ya janyo musayar wuta tsakanin su da wani gungun masu garkuwa da mutanen, inda ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutum ɗari, ciki kuwa har da mata da yara ƙanana.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan rikici ya faru ne tsakanin gungun Mani sarki da na Ɗanƙarami wanda ke da goyon bayan Gungun Abu Rada. Shi dai Sarki Mani wanda a da tsohon mai garkuwa da mutane ne, wanda ya ajiye makaman sa ya tuba da wannan sana’a ya kuma koma garin Illela da zama. Wannan tuba da ya yi bai wa abokan sana’ar ta sa daɗi ba, a dan haka suke kallon sa a matsayin wanda ya ci amanar su. Sai dai ance wasu daga cikin yaran sa sun ƙi amincewa da wannan yarjejeniya ta tsagaita wuta, dan haka suka ƙi amincewa da su bi shi su koma cikin jama’a su zauna.

Ana cikin wannan hali ne, sai wasu daga cikin gungun Ɗanƙarami suka shirya kai wa garin Illela hari, a wannan , a lokacin da suka kai wannan hari sai ya kasance tuni su Mani sun samu labara, dan haka su ka yi musu kwanton ɓauna suka bude musu wuta. Inda Allah ya ba su nasara a kan su Ɗan Da suka fatattake su. Garin gudu har suka zubar da da yawa daga makaman su, inda su kuma su mani suka kwashe. Wadannan makamai sun haɗa har da manyan bindigogi masu kakkaɓo jiragen yaƙi, wanda hakan bai musu daɗi ba, kuma suka sha alwashin sai sun ɗau fansa.

Rahotanni sun nuna dama kuma akwai wata jiƙaƙƙa a tsakanin ɓangarorin guda biyu, domin kuwa a lokacin da Mani ke zaman daji ƙanin sa ya taɓa yin garkuwa da wata matar ɗaya daga cikin abokan adawar ta su, har sai da aka biya shi zunzurutun kuɗi har Naira 500,000 sannan ya sako ta. Wannan ma na cikin dalilan da ta saya suke ta hakon su kama ɗaya daga cikin su.

A yayin wannan arangama dai da a ka yi, ance ɗaya daga cikin ƙannen Sarki da ake kira Chirwa tare da matar sa sun rasa rayukan su, kuma wasu ƙannen nasa su huɗu da suka haɗa da Kabiru, Tanimu da Sulaiman sun samu raunuka kuma a yanzu suna asibiti a Katsina rai ga hannun Allah. Waɗannan dalilai na cikin abubuwan da suka ƙara ƙarfin gaba a tsakanin gungun biyu.

Haka kuma ance zaman mani a Illela ya zamarwa mutanen yankin wata kariya, domin ya sha raraka sauran gungunan a duk lokacin da su ka yi yunƙurin afka wa ƙauyukan wannan yanki. Hakan ya sanya su ka ga dole su haɗa kai su kawar da shi, shi kuma ya tsaya kai da fata akan sai dais hi ya ga bayan su. Haka kuma rahotanni sun tabbatar da cewar zaman Mani a wannan yanki, ya kuma hana su kai shanun su yankunan da suke makwabtaka da qauyukan da yake zaune, duk kuwa da suna da yalwar makiyaya da mashaya da makiyayi zai so ya kai dabbobin sa su yi kiwo.

A saboda haka rahotanni suka tabbatar da cewa wasu gungu guda uku da suka haɗa da na Ɗanƙarami, Ɗangwate da na Maikomi suka haɗa kai domin zuwa ɗaukar fansa a kan Alhaji Mani da sauran yan gungun sa da suke tare da shi, dan haka a daren Talata ta wannan makon, wannan gungu guda uku suka yi wa garin an Illela takakka da nufin ɗaukar fansa, da kuma ƙwato makaman su da suke hannun su Alhaji Mani. Wasu mazauna garin sun ce yawan su ya haura mutum 300 kowanne ɗauke da mugun makami.

A yayin da suka yi wa garin tsinke, suka fara kan mai uwa da wabi da alburusai a kan mutanen garin. Sai dai kuma ba su san da cewa tuni Sarki da yarn sa sun samu labarin abin ba tun ba yau ba, dan haka dama sun shirya musu, sun musu kwanton vauna. Inda su ka yi nasarar tarwatsa gungun na su na haɗin guiwa, su ka kuma fafare su, dalilin da ya sanya su ka bi su har mavoyar su, inda ka yi balahira aka kashe mutane da dama, wasu kuma da dama suka samu raunuka. Wannan balahira dai ta yi wa mutane mazauna wannan yanki da dama daɗi, an ce anga mutane suna ta nuna farin cikin su akan wannan abu da ya faru.

To amma kuma wani rahoton da ke fitowa daga baya bayan nan, ya nuna cewa fa ba wai waɗancan dalillan ne kawai suka jawo wannan arangama ba, wasu mutane mazauna wannan yanki suna ganin wannan kawai rigima ce tsakanin waɗanda suke so a yi sulhu da gwamnati da waɗanda suke ganin sun yi wa sana’ar zuwan sojan badakkare. Sai dai wasu daga cikin su suna ganin ai da ma ba shiga suka yi dan su dauwama ba, da ma sun shiga wannan sna’a ne domin an take musu hakkin su, kuma in dai har gwamnati na da niyyar ta sasanta da su ta ƙwato musu hakkin su, to suna ganin za su iya barin wannan sana’a. Wannan shi ne ra’ayin irin su Alhaji Mani.

A wannan ƙaulin kuma an ce bayan ritayar da Alhaji Mani ya yi ya kuma koma ƙauyen Illela da zama, abokan sana’ar ta sa sun lura bai miƙa wa gwamnati makaman sa ba, kuma sun yi imanin cewa yana da makamai masu yawa da kuɗin su zai iya kaiwa kimanin Naira 5,000,000 koma su fi, wannan ce ta sanya suka durfafi garin da shirin su afka masa su kama shi domin ya nuna musu inda ya ɓoye makaman sa da bai miƙa wa hukuma ba. Wannan ne ya sanya da suka shiga garin suka fara bincike gida gida suna neman sa, a yayin da shi kuma tun da ya samu labarin zuwan su, ya haure tare da yaran sa ya bar garin. To amma kuma an ce da ya fita wuri ya samu da yaran sa ya laɓe ya tare musu hanya, dalilin da ya sanya bayan sun shiga garin, suka ringa bi gida gida su na neman sa. A wannan binciken da suke ne, har suka shiga gidan Sarkin Fawa Mu’azu, a nan kuma suka samu wata bindiga ta maharba, ganin wannan bindigar ta sanya su ka zargi sarkin fawa da cewa yana cikin yan ƙato da gora da ke kai musu farmaki, dan haka suka kashe shi, duk kuwa da ya tabbatar musu shi ba ɗan bijilenti ba ne.

Bayan komawar su ne, suka yi wannan arangama, inda suka buɗe wa junan su wuta ba ji ba gani, inda suka halaka sama da mutum ɗari a junan su, suka kuma raunata da dama. Cikin waɗanda suka samu raunuka har da shi Ɗanƙarami wanda shi ne uban gayyar, wanda aka ce an harbe shi a hannu. Da aka tambayi mutanen garin, ko sun sanar da jami’an tsaro wannan abu da ya faru? Sai suka ce ai da yake sun san rigima ce a tsakanin su, jami’an tsaro sun bar su ne su kashe kan su.

Wani wanda Jaridar Manhaja ta zanta da shi ya ce an dai yi dambun gawa a dajin amma a gaskiya ba zai iya cewa ga yawan mutanen da aka kashe ba.

Kakakin Rundunar ‘Yansandan Jihar Katsina ASP Gambo Muhammed da manema labarai suka lalube shi a kan batun, sai ya kada baki ya ce “Muna nan muna bincike a kan abin.”

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*