Waɗanda suka yi garkuwa da tsohon Mataimaki Gwamnan Jihar Nasarawa, Farfesa Onje Gye Wado, sun bauƙaci a biya su Naira miliyan 70 kafin su sako shi.
Binciken Manhaja ya gano a ranar Juma’a masu garkuwar suka yi magana da ahalin wanda ke hannunsu don neman kuɗin fansa.
Sai dai majiya ta kusa da Wado ta ce ‘yan uwansa sun nemi rage a wajen ‘yan bindigar kan su biya Naira miliyan biyu don a sake shi.
‘Yan uwan nasa sun nuna damuwa saboda a cewarsu, hutun gama-gari da ake yi zai hana zuwa banki don tattaro kuɗin da suke buƙata.
“Masu garkuwar sun yi magana da ‘yan uwan Farfesan inda suka buƙaci a biya su Naira miliyan 70, amma ahalin nasa suka ce a yi musu ragi zuwa Naira miliyan biyu,” kamar yadda majiyar ta shaida wa jaridar Vanguard.
Da safiyar ranar Juma’a ‘yan bindigar suka yi garkuwa da Farfesa Onje Gye-Wado a gidansa da ke ƙauyen Gwagi a yankin Ƙaramar Hukumar Wamba a jihar.