Masu garkuwa sun fito da sabuwar dabarar sanya kayan makaranta don yin garkuwa da ɗalibai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Jihar Oyo a ranar Juma’a ta shelanta cewar masu garkuwa da mutane sun fara shigar burtu, suna saka kayan makaranta domin sace ɗalibai a Ibadan, babban birnin jihar.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da aka raba wa masu ruwa da tsaki a ranar 27 ga Oktoba, 2021, wacce ta fito daga Ofishin Sakataren Dindindin na Ma’aikatar Ilimi, Kimiyya da Fasaha ta Jihar Oyo.

Takardar wadda aka tura wa Shugabannin Hukumar Ilimi Matakin Farko (SUBEB) da TESCOM da kuma Babban Sakatare na Hukumar BOTAVED, daraktoci da kuma masu sanya ido a harkokin ilimi na kananan hukumomi, shugabannin makarantun sakandare da na firamaren gwamnati da na kuɗi, tare da masu makarantun kuɗi da iyayen yara.

A cewar sanarwar, wata sabuwar hanya ce da masu garkuwa da mutanen suka fito da ita don satar yara, saboda ake kira ga iyayen yara da su ja kunnen ‘ya’yan su da su guje wa mutanen da ba su sani ba da sunan za su hau ababen hawansu domin rage mu su hanya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *