Masu garkuwa sun sace tsohon Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi, Okey Wali

Wasu da ba a san ko su wane ne ba sun yi garkuwa da tsohon Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi ta Nijeriya (NBA), Okey Wali, a Jihar Ribas.

Manhaja ta kalato an yi garkuwa da Wali ne biyo bayan harin da aka kai wa tawagarsa da safiyar Litinin a yankin Ƙaramar Hukumar Obio/Akpor a jihar.

Kakakin ‘yan sandan Ribas, Grace Iringe-Koko, ita ce ta tabbatar da faruwar hakan.

Jami’ar ta ce ‘yan sanda na bakin ƙoƙarinsu don kuɓutar da Wali cikin ƙoshin lafiya.

Ta ce, “Muna sane da batun. Ya faru ne a kusa da yankin Obiri Ikwerre. Muna bincike don tabbatar da an kuɓutar da shi.”

Kawo yanzu Ƙungiyar Lauyoyi ta Nijeriya (NBA), ta roƙi masu garkuwar da su saki tsohon shugaban nata ba tare da ya ji ko ƙwarzane ba.

NBA ta yi wannan kira ne a ranar Talata ta bakin Shugabanta, Yakubu Maikyau, SAN.

Maikyau ya yi kira ga hukumomin da lamarin ya shafa da masu ruwa da tsaki da su ba da himma wajen ganin Wali ya shaƙi iskar ‘yanci.