Masu haƙar albasa suna buƙatar tallafin gwamanti don bunƙasa harkokinsu – Dakta Isma’la Jibiya

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Dakta Isma’la Ɗan Nuhu Jibiya, mataimakin shugaban ƙungiyar albasa na ƙasa ya bayyana cewa, albasa ta kasance wani kayan gona mai matuƙar muhimmanci don haka Hausawa ke karin magana ma na cewa ‘kada a yi tuya a manta da albasa’.

Dakta Isma’la ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da ’yan jarida a yayin taron shiyyar Afrika kan hada-hadar Albasa da aka gudanar na kwanaki biyu a ɗakin taron na Gidan Gwamnatin Kano.

Ya ƙara da cewa, ba bu gidan da ba a amfani da Albasa a duniya, wanda hakan ya sanya Albasa ta yi farin jini sosai.

Ya ce, don haka a matsayinsu na ƙungiyar ’yan albasa suka ga ya kamata su tsaya su ga wane ƙalubale albasa ta ke da shi su kuma magance, don haka suka taru a Jihar Kano suka tattauna matsaloli na Sufuri akan albasa, me yasa take tsada kafin ta kai inda za ta kai, kuma me yasa wani lokaci ake sayenta N6,000 buhu Sannan watanni huɗu zuwa Biyar a saye ta N80,000 zuwa 90.

Waɗannan dalilai da suka tara su, daga cikinsu akwai maganar wurin ajiya albasa mai kyau wanda ba su da shi, wannan in sun samar da shi zai rage musu asarori na albasa da kuma duba wacce hanya za su bi dan wadatarda albasa a ƙasa da ake da buƙatar samar da tan Miliyan biyu da 500 amma yanzu tan Miliyan ɗaya da 500 kawai suke iya samarwa, ya ya za a yi su cike wannan gurbin, duk suna daga abinda suke son cimma a taron.

Dakta Isma’il ya ce, taron ya haɗa manoman albasa da ’yan kasuwa ma su sayar da ita, akwai masu sarrafata, da kowa a watse yake, manomi ba ruwansa da ɗan kasuwa, ɗan kasuwa ba ruwansa da mai sarrafawa, kowa yana harkar sa akan kansa.

Sun haɗu ne a yanzu waje ɗaya saboda kowa nada ƙalubale, sai an haɗu waje ɗaya za’a iya warware ƙalubalen, don haka ƙungiyar ta haɗa su gaba ɗaya, yanzu manomi ba zai yi ba sai da ɗan kasuwa, ɗan kasuwa sai da mai sarrafawa, saboda haka yanzu akwai alaƙa mai ƙarfi tsakaninsu.

Ya ci gaba da cewa, zuwa yanzu dai ba wani tallafi da ’yan albasa suka samu daga  Gwamnati, don haka suna kira ga Gwamnati kamar yadda suka ji ana cewa, tana bai wa manoma tallafi basa biya, suna so a ba manoman albasa a gani saboda shi manomin albasa dama harkar ta yake, ba abune da za a noma a ajiye ba, abune da in an ba shi kuɗin harkar albasar zai yi.

Kuma har yanzu Gwamnati ba ta ce komai a kansu ba, amma sun san da yardar Allah da taimako da mai girma Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ba su na gudummuwa a wannan taro da suka yi a Kano, ta ɗaukar nauyin dukkan wurare da suka yi taron da yi musu hidima, da yi musu alƙawura daban-daban ta bakin mataimakinsa kwamishinan noma na Jihar kano Dakta Nasir Yusuf Gawuna sun tabbatar, ba za su kyale wannan jinjirar ƙungiya ta albasa, ta yi kuka ba.

Ya ja hankalin ’yan ƙungiyar da su yi amfani da dukkan abubuwa da aka tattauna a taron na Kano su yi  aiki da shi don bunƙasa cigaban harkokinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *