Masu kwarmato ke da alhakin sace Janar Tsiga – Shugaban Ƙaramar Hukumar Bakori

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina.

Shugaban ƙaramar hukumar Bakori, Alhaji Ali Mamman Mai Citta Bakori, ya faɗi haka a sa’ilin da ya ke zantawa da manema labarai a ofishinsa.

Ya ce, yawancin satan mutane da ta’adanci na faruwa ne da taimakon informers a ƙaramar hukumar na Bakori da sauran ƙananan hukumomin da ke fama da rashin tsaro

Amma ya bayyana cewa haɗin gwiwa jami’an tsaro da jami’an ƙaramar hukumar na yin iyakar ƙoƙarin sun wajen kuɓutar da Janar Tsiga.

Sai dai ɗaya daga cikin yan uwan Birgediya Tsiga wanda bai so a faɗi sunan sa, yace ɓarayin dajin sun bukaci a biya Naira miliyan 250 kafin su sake Janar Tsiga mai ritaya.

Har yanzu dai babu wani bayani daga ‘yan bindigan ko jami’an yan sanda a jihar.

Shugaban ƙaramar hukumar ya kuma bayyana wasu matakai da gwamnan ya ɗauka a jihar da yace yayi tasiri ƙwarai wajen samun zaman lafiya.

“Babu shakka samar da jami’an tsaron al’umma CWC guda 150 da wadata su da kayan aikin ta’adanci a ƙaramar hukumar ta Bakori”Mamman Citta.

“Haka kuma ƙaramar hukumar ta ɗauki ‘yan sintiri guda 100 da take ba kowanne su alawus na dubu goma a duk wata domin su taimaka wa sauran jami’an tsaron da ke samar da tsaro a yankin”ya faɗi haka.

Ya bayyana malam Dikko Raɗɗa ya kawo romon dimokuraɗiyya a kowane lungu da ke faɗin jihar.