Masu ruwa da tsaki sun buƙaci bincike kan zargin USAID da ɗaukar nauyin Boko Haram

Daga BELLO A. BABAJI

Wasu ƴan Nijeriya sun buƙaci a gudanar da bincike game da zargin da wani ɗan majalisa a Amurka mai suna Scott Perry ya yi na cewa Hukumar Tallafa wa Ci-gaban Ƙasa-da-ƙasa ta Amurka (USAID) tana ɗaukar nauyin ƙungiyoyin ta’addanci ciki har da Boko Haram.

Perry, wanda ɗan jam’iyyar Republican ne da ke wakiltar Pennsylvania ya yi ikirarin haka ne a yayin zaman ƙaddamar da Ƙaramin Kwamitin Cimma nasarorin Gwamnati a ranar Alhamis.

An gudanar da zaman ne musamman don warware matsalolin ware kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba da ayyukan badaƙala, wanda ya mayar da hankali akan zargin kashe kuɗaɗen haraji ta hanyoyin da suka saɓa wa doka.

A ƴan kwanakin nan ne Shugaba Trump ya dakatar da USAID da wasu shirye-shirye na agaji bisa zargin su da rashawa.

Ba’amurken ɗan majalisar ya zargi USAID ne da ɗaukar nauyin ƙungiyoyin ta’addanci inda ta ke ware masu Dala miliyan 697 a kowacce shekara.

A wani bidiyo da ya karaɗe kafafen labarai, Perry ya lissafo ƙungiyoyin kamar haka; ISIS, Al-Qaeda, Boko Haram da ISIS Khorasan da wasu sansanonin horar da ta’addanci.

Hakan na zuwa ne a lokacin da hukumomin Nijeriya suka koka game da su waye ke ɗaukar nauyin ta’addancin mayaƙan Boko Haram da makamantansa.

A wata hira da Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Christopher Musa da tashar Al-Jazeera, an ga inda ya nuna damuwa game da yadda ƙungiyoyin ƙasa-da-ƙasa masu zaman kansu suke gudanar da ayyukansu a yankunan da ke fama da matsanancin rashin tsaro musamman a Arewa maso Gabas da Boko Haram da ISWAP suka addabi al’umma.

Ya yi kira ga Majilisar Ɗinkin Duniya da ta gudanar da bincike game da waɗanda suke ɗaukar nauyin ƙungiyoyin ta’addanci, ya na mai cewa sojoji sun kama da dama daga cikin ƴan ta’adda ɗauke da kuɗaɗen ƙasashen waje.

Wasu daga cikin waɗanda suka koka game da al’amarin sun haɗa da tsohon jakadan Nijeriya ga Brazil, Dele Cole, da tsohon ministan ilimi, Farfesa Tunde Adeniran da kuma wasu jami’an harkokin ƙasashen waje.