Masu safarar itatuwa da gawayi sun ce sun dawo da ƙarfinsu bayan gwamnatin Nijeriya ta ɗage musu takunkumi

Daga AMINA YUSUF ALI

Bayan gwamnatin tarayya ta ɗage musu takunkumin fita da hajarsu ƙasashen ƙetare, masu safarar gyararrun gungumen itatuwa da gawayi sun yi kira da a zo a sanya musu hannayen jarin Dalar Amurka biliyan 152.94.

‘Yan kasuwar sun lashi takobin haɓaka jarin kasuwancinsu har zuwa Dalar Amurka biliyan $152.94 a wannan shekara ta 2023.

Bayan gindaya musu sharuɗɗa, gwamnatin tarayya ta ɗage takunkumi a kan safarar gawayi da guma-guman itace domin ta taimaka wa kasuwancin, musamman ma waɗanda suke gyara shara ta koma dukiya domin havaka hada-hada tsakanin Nijeriya da ƙasashen duniya.

Ministan Muhalli na Nijeriya, Mohammed Abdullahi, shi ya bayyana haka a Abuja a taron tuntuɓa na a kan bitar takunkumin safarar itace da gawayi.

Abdullahi ya ƙara da cewa, Ma’aikatar tasa ta kula cewa, akwai wasu kasuwanci da aka daƙile ba tare da sani ba, musamman waɗanda suke gyara shara ta zama dukiya, kuma aka sa musu takunkumi ba tare da sani ba.

A matsayinsu na gwamnati mai tunani bai kamata su zama marasa tanƙwaruwa ba a kan dokoki. Kuma kullum a shirye suke don saurarar ‘yan ƙasa game da yadda wasu dokokin suka zamar musu takura.

Wannan ya sa a cewar sa, bayan nazari mai kyau, yake ba da sanarwar ɗage takunkumin safarar itace da gawayi amma a bisa wasu sharuɗɗa.

Abdullahi, ya qara da cewa, wannan ɗage takunkumi zai iya zama wata dama ga kamfanoni da mutane su shigo a dama da su a harkar shuke-shuke don cin riba a gaba. Sannan ya nemi ‘yan kasuwar su kiyaye dokokin sare itatuwa don gudun shiga komar hukuma.

Shi ma Daraktan gudanarwa na Hukumar Safarar kaya ta Nijeriya, (NEPC), Dakta Ezra Yakusak, ya yaba wa gwamnati da cire takunkumin sannan ya gargaɗi masu safarar da su kasance masu biyayya ga dokoki in dai har suna son cigaba da bunƙasar kasuwancinsu.

Daga ƙarshe, Yakusak ya bayyana cewa, hukumarsu a shirye take don tallafa wa ‘yan Nijeriya da suke son yin harkar safara, za su ba da gudunmawar da ta kamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *