Masu sayen ƙuri’a sun kai wa jami’an EFCC hari a Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

An kai wa jami’an EFCC hari a yayin da suka ƙara matsa lamba kan aikin sanya idanu a zaɓen da ake gudanarwa na gwamnoni da ’yan majalisun jihohi.

Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce, an kai wa jami’an nata hari ne a Unguwar Rimi yayin da suke yunƙurin kama wasu da ake zargi da sayen ƙuri’a.

Tawagar tasu da ke aikin sanya idanu na sirri ta yi zargin wani mutum da ake kira Kabiru Musa da aka gani cikin wani bidiyo riƙe da wayarsa yana aikawa mutane kuɗi idan suka kaɗa ƙuri’arsu, abin da ya sanya suka kai samamensu yankin ke nan domin su kama shi.

Da zuwansu suna ƙoƙarin kama shi, sai musa ya sanya ihu wanda tamkar alama ce ga abokan aikisa cewa yana cikin matsala.

“Sun yi amfani da makamai kan jami’anmu abin da ya kai ga raunata wasunsu. Ya ɗauke su dogon lokaci suna fafatawa da matasan, saboda dagewar da suka yi sai sun kama wanda suke zargi.

“Bayan sun sanya wanda suke zargi a mota, sai aka fara jifan motar da manyan duwatsu da sauran abubuwa abin da ya sanya aka jikkata ma’aikatanmu uku kenan,” in ji sanarwar.

Waɗanda aka raunatan yanzu haka suna karɓar kulawa a wata cibiyar lafiya da ke Kaduna, kuma wanda ake zargin yana hannu har zuwa a kammala bincike.

An kai wa ma’aikatan EFCC makamancin irin wannan hari a yayin zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana, aka kuma lalata abun hawansu.