Masu zabiya na buƙatar kulawa ta musamman daga gwamnati – Shugaban Ƙungiyar Zabiya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban Ƙungiyar Zabiya ta Nijeriya (AAN), Jake Epelle, a ranar Talata ya roƙi gwamnatin tarayya da ta jihohi kan shirin magance cutar kansar fata ga masu fama da zabiya (PWA).

Epelle ya yi wannan roƙo ne a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya a Kalaba.

Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya masu hali da ƙungiyoyi da su taimaka waasu fama da zabiya.

Shugaban ya ce, illar cutar kansar fata tana kashe masu zabiya kuma dole ne a yi wani abu don shawo kan cutar.

Shugaban ya ƙara da cewa, matakin da aka ɗauka na kula da masu fama da wannan cuta bai kasance mai kwarin gwiwa ba tsawon shekaru duk da cewa sun kasance cikin aiwatar da yarjejeniyar da Gwamnatin Tarayya ta yi da su.

“Buƙatunmu ba su wuce buƙatun wasu ba. Wazannan sun haɗa da maganin kansar fata kyauta, ingantaccen ilimi, haɗa kai da zamantakewa da kuɗi.

“Akwai ƙalubalen kyama, nuna wariya, cin zarafi, rashin mutunci, da kuma ƙunar rana a jiki yana ɗaya daga cikin matsaloli masu tsanani saboda yana iya ƙara haɗarin kamuwa da cutar kansar fata”, inji shi.

A nasa ɓangaren, Bassey Mbang, shugaban gudanarwa na ƙungiyar ta Kuros Riba ya ce, muryar PWA a jihar ta ragu matuƙa saboda da ƙyar ake gane su.

Mbang ya ce, babu wanda ke son duba ƙalubalen masu fama da wannan cuta, ta yadda hakan ke sanya rayuwarsu cikin wahala da kuma jefa su cikin haɗarin kamuwa da cutar kansar fata.

“A Kuros Riba muna da mutane kusan 800 da ke fama da cutar zabiya a ko’ina a faɗin jihar kuma ƙalubalen shi ne tattara kowa da kowa domin yana da babban jari.

“Don haka, saboda rashin haɗin kai, ba za mu iya samar da wayar da kan da ake buƙata ga mutanen da ke da zabiya don taimaka musu su san yadda za su magance yanayin ba.

“A yanzu haka, muna da mutane tara da ke fama da cutar sankara ta fata, don haka, muna amfani da wannan damar wajen bayar da shawarar cewa a farfaɗo da shirin kula da cutar daji da Gwamnatin Tarayya ta yi wa masu fama da zabiya.

“Muna kuma kira ga mutane da ƙungiyoyi masu zaman kansu da su taimaka mana, ba dole ba ne taimakon ya kasance a cikin tsabar kuɗi, muna buƙatar inuwar rana, laima da yaƙin wayar da kan jama’a,” inji shi.

NAN ta ruwaito cewa, zabiya cuta ce ta ƙwayoyin halitta wacce ke haifar da raguwar samar da wani launi mai suna ‘melanin’ a cikin fata, gashi da idanu wanda ke haifar da haske ko launi.

Melanin yakan kare fata daga lalacewa saboda fallasa hasken ultraviolet.

Mutanen da ke da zabiya sun fi fuskantar fallasa daga rana; Hakanan suna da haɗarin kamuwa da cutar kansar fata tun daga farkon shekarun samartaka.

Bayanai da ake samu sun nuna cewa a yankin kudu da hamadar sahara, zabiya na shafar mutum ɗaya a cikin kowane 2,000 zuwa 5,000, mutane, yayin da a wasu ƙungiyoyi, adadin ya kai ɗaya cikin mutane 1,000.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *