Masu zanga-zanga sun garƙame Ministan Ayyuka a ofishinsa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wasu ma’aikatan da suka yi zanga-zanga sun kulle Ministan Ayyuka da Gidaje na Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Mista Dave Umahi, a cikin ofishinsa da ke Abuja.

An ce ministan ya hana ma’aikatan da suka zo aiki a makare samun damar shiga ma’aikatar.

’Yan ƙungiyar da suka hada da ma’aikatar gidaje da ayyuka sun yanke shawarar kulle ma’aikatar, tare da hana shiga da fita da kuma hana ministan fita daga ofishin.

Sun kuma yi ikirarin cewa ya hana injiniyoyi da daraktoci yin aikinsu, kuma tun bayan naɗa shi ya ke karya ƙa’idojin aikin gwamnati, ta hanyar kawo masu ba da shawara don tafiyar da harkokin ma’aikatar.

A cewar AIT, jami’in ƙungiyar, Williams Kudi ya ce ministan ta ƙi ba su dama su bayyana damuwarsu.

Kawo yanzu dai ba a kai ga samun ministan da muƙarrabansa ba.