Masu zanga-zanga sun karɓe harabar Majalisar Tarayya

Daga BASHIR ISAH

Mambobin ƙungiyar ƙwadago da ke gudanar da zanga-zanga a Abuja sun karɓe harabar Majalisar Tarayya a ci gaba da zanga-zangar tasu da suka fara a ranar Laraba.

Majiyarmu ta ce masu zanga-zangar sun karɓe harabar majalisar ne jim kaɗan bayan da sanatoci suka shiga ganawar sirri.

Ta ƙara da cewa, sun samu shiga harabar Majalisar ne bayan da suka ɓalle babbar get ta ɗaya da ta biyu na shiga harabar.

NLC da dangoginta sun fara zanga-zanga ne domin nuna adawarsu dangane da matsin rayuwar da suka ce gwamnati ta jefa ‘yan ƙasa ciki sakamakon cire tallafin mai.

Ƙungiyar ta ƙaddamar da zanga-zangar ne a Abuja inda bayan haka rassanta na jihohi su ma suka bi sahu.

Ya zuwa haɗa wannan labarin, ana sa ran Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya fito ya yi wa taron masu zanga-zangar jawabi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *