Mata ba su da wata rawa da suke takawa a masarautun Ƙasar Hausa – Gimbiya Umma Usman Nagoggo

“Akwai buƙatar a dawo wa da sarakuna ƙarfin mulkin da suke da shi a baya”

Shafin Gimbiya na wannan makon ya lalubo muku Gimbiya ce ta gaske, domin kuwa tana daga cikin ýaýa 42 da tsohon Sarkin Katsina marigayi Usman Nagoggo ya haifa, wato Hajiya Umma Hassan, ýar uwa ga marigayi Janar Hassan Usman Katsina, tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Arewa. Gimbiya ýar sarki, matar sarki, kuma uwar sarki, wacce ta shafe tsawon shekaru tana hidima ga al’umma da taimakon raunana, kuma mamba a Jam’iyyar Matan Arewa. A zantawarta da wakilin Blueprint Manhaja Abba Abubakar Yakubu, Gimbiya Umma Hassan ta bayyana yadda ta taso a gidan sarauta, tarbiyyar da ta samu da kuma burin ta kan samar da cigaban tsarin sarautun gargajiya a Nijeriya. A yi karatu lafiya.

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

MANHAJA: Ko za ki gabatar mana da kan ki?
HAJIYA UMMA: Sunana Hajiya Umma Hassan. Ni ýa ce ga tsohon Sarkin Katsina marigayi Usman Nagoggo. Ina da shekaru 60 a duniya, na taso a gidan sarauta. Kamar yadda yake bisa al’adar gidanmu, kuma al’adar ýaýan Hausawa, muna farawa ne da karatun allo, sannan a sa mu firamare, zuwa sakandire. Na yi karatu a Kwalejin Horar da Malamai Mata ta Katsina wato WTC, daga nan kuma aka yi min aure. Na auri ɗan uwana tsohon Sarkin Fawwa wato Sarkin Ƙanƙara marigayi Lawan Areda, kuma Allah ya albarkace mu da ýa’ya biyar, daga ciki akwai tsohon Sarkin Fawwa wanda ya gaji sarautar mahaifinsa, Yusuf Lawan.

Yaya rayuwa take a tsakanin ku ýaýan Sarki, lokacin tasowa?
Rayuwa a wancan lokacin ta fi daɗi sosai, domin hankali a kwance yake babu ruɗani irin na yanzu. Mun taso cikin kyakkyawar rayuwa, da haɗin kai. Mahaifinmu ya ba mu kulawa ta musamman, cikin kyakkyawar tarbiyya da mutunta juna.

Shin akwai wata tarbiyya ta musamman da ýaýan sarakuna ke samu game da jagorancin al’umma?
E, ƙwarai. Kamar yadda na faɗa a baya mun samu kyakkyawar tarbiyya da muka tashi da ita, domin mu bamu san yin alfahari wai don muna gidan sarauta ba, dukkanmu da kowa ɗaya ne. Mahaifinmu ba ya nuna bambanci tsakaninmu da yaran gida komai tare muke yi.

Wacce gudunmawa mata ke bayarwa wajen tafiyar da harkokin fada?
E, to. Ai da yake mu a Ƙasar Hausa ko in ce Ƙasar Katsina mata ba su da wata rawa da suke takawa a harkokin fada, sai dai idan kina auren basarake ana iya ba ki sarautar Fulani, Magajiya, ko Gimbiya. Amma game da abin da ya shafi tafiyar da mulki wannan na maza ne.

Shin kina ganin ya kamata a bai wa sarakuna wani matsayi na musamman a ƙarƙashin kundin tsarin mulkin ƙasa?
Wannan kam gaskiya abu ne mai kyau. Ina goyon bayan hakan, idan gwamnati za ta duba irin ɗimbin gudunmawar da sarakuna suke bayarwa wajen duba sha’anin al’umma, akwai buƙatar a dawo musu da ƙarfin ikon da suke da shi a baya, ta hanyar sanya shi a cikin kundin mulkin ƙasa, hakan zai ƙara musu ƙima da daraja, kuma ya sa jama’a su ƙara bai wa gwamnati haɗin kai sosai. Ina fatan Gwamnati za ta ƙara kulawa da al’amarin sarakuna sosai a dukka cikin aikin ta, domin shawarar sarakuna ita ce mafi amfani, saboda su ne suka fi sanin ciwon talakawansu.

Wanne fata kike da shi nan gaba ga matsayin ýaýan sarakuna wajen gina ƙasa?
Ina fatan ganin ýaýan sarakuna masu tasowa za su mayar da hankali wajen yin karatu mai zurfi, kuma su shiga gwamnati a dama da su, don su samu damar ba da tasu gudunmawa ga cigaban ƙasa, ba lallai sai a cikin fada ba. Sarauta gadonmu ce, da Allah ya ƙaddara rayuwarmu a cikin ta, kuma hakkin mu ne mu kula da amanar talakawa da ke ƙarƙashin masarautunmu, ba dole sai lokacin da mulki ke hannun mu ba. A baya ɗan’uwa na marigayi Janar Hassan Usman Katsina ya shiga gwamnati saboda kasancewarsa a aikin soja, bayan sa ma akwai wasu da dama da suke ayyuka daban daban har da likitoci.

Yaya dangantakar ki take da sauran ƙungiyoyin mata na Arewa?
Alhamdulillahi. Akwai dangantaka ta girmamawa a tsakanina da mata masu harkokin ƙungiyoyi na cigaban mata da taimakawa raunananu. A duk lokacin da wata buƙatar tallafawa ta tashi, ina yin duk abin da ya kamata, gwargwadon abin da Allah ya hore. Sannan kuma a ɗaya ɓangaren ina tare da Jam’iyyar Matan Arewa, da ke ƙoƙarin kare muradun mata da inganta rayuwar su. Duk da yake dai ba wani matsayi ne da ni a ƙungiyar ba, amma muna ba da shawarwarin da suka kamata, don samar da cigaba.

Idan za a baki dama wanne abu kike so ki yi don kawo canji a ƙasar nan?
Babu abin da ya fi tsaya min a rai kamar game da al’amarin ƙasar nan kamar matsalar taɓarɓarewar tsaron da ake fama da ita a Arewa da ma wasu sassan ƙasar nan, musamman mu a nan Katsina da matsalar ýan bindiga da sace sacen mutane ta addabe mu. Don haka babu abin da nake so na ga an samu canji a kansa irin yadda za a samu nasarar kawar da wannan matsalar bakiɗaya.

Wanne abu ne kika fi yi lokacin da kike buƙatar shaƙatawa ko ɗebe kewa?
A lokacin shaƙatawa na fi son in kaɗaice ina yin tasbihi ko karatun Alƙur’ani ko kuma in zauna ina kallon talabijin.

Wanne abu ne za ki so a riƙa tunawa da ke a kansa?
To, ni dai ina son a riƙa tunawa da ni a saboda koƙarin da nake yi wajen aikin zumunci, domin kuwa ina son ýan uwana sosai. Babu lokacin da na fi samun farin ciki da nishaɗi kamar lokacin da nake cikin dangina ana zumunci.

Na gode kwarai, Hajiya.
Ni ma na gode sosai.