Mata mu dage mu nema wa kanmu ‘yanci ta hanyar ilimi da sana’o’i – Hauwa Umar

“Ilimina ne babban nasarata a rayuwa”

Daga BABANGIDA S.GORA KANO

Sanin kowa ne halin da duniya ta ke ciki yanzu, babu wanda ake yi da shi face wanda ya tashi tsaye wajen ganin ya yi wani yunƙuri na azo a gani, wannan ne ya sa su ma mata ba su bari an bar su a baya ba ta hanyar kutsawa don su ma a dama da su. Wannan ne ya sa shafin mata A Yau yake zaƙulo ire-iren su don jinjina wa namijin ƙoƙarin da suke yi tare kuma da zama wata makaranta ga mata masu tasowa. A wannan sati mun zakulo wa masu karatu ɗaya daga cikin irin matan da suka kasance abin koyi. Hajiya Hauwa Umar Aliyu, mace ce mai kamar maza, ‘yar gwagwarmaya da har ta kai matsayin mai ba wa gwamnan Jihar Jigawa shawara kan harkokin mata. A tattaunawarta da Blueprint Manhaja, za ku ji tarihin rayuwarta da kuma yadda ta kai matsayin da ta ke kai. A sha karatu lafiya:

BLUEPRINT MANHAJA: Mu fara da jin tarihinki a taƙaice.

HAUWA: To, Assalamu alaikum. Sunana Hauwa Umar Aliyu (Hauwa Birniwa),‘Yar Ƙaramar Hukumar Birniwa ce a Jihar Jigawa. Ni Bafilatana ce daga Ruga, Yayar mahaifina da ke zaune a Kano ta ɗauke ni ta tafi da ni Kanon, A hannun ta na girma.

Ya batun karatu?

Kafin a kawo ni Kano, na fara karatun addini gaban mahaifiyata a nan rugarmu, na yi karatuna tun daga firamare har zuwa jami’a a garin Kano. Na yi digirina na farko a ɓangaren ‘Education Islamic Studies’, bayan kammala karatu, na yi bautar ƙasa a Kano, daga nan na koma jiharmu ta Jigawa inda na fara aikin koyarwa.

Na fara aikace-aikace na aikin sa-kai na ƙungiyoyi wanda daga ciki na samu damar zama daraktan tsare-tsare ta ƙungiyar miyatti a jiharmu ta Jigawa. Bayan digirina na farko, na je Kenya, na yi ‘Postgraduate Diploma’ a vangaren lafiyar mutanen karkara (Community Health) da na gama na dawo gida, na ci gaba da aiki wanda ya haɗa da aiki da ƙungiyoyi na ƙasashen waje. Sai kuma na sake koma wa karatu.

Na sake yin ‘Postgraduate Diploma in Education, Health Promotion and International Development’ a Institute of Education (IOE) da ke Jami’ar University College London (UCL) da ke Ƙasar Biritaniya. Na kuma yi ‘masters’ ɗina (Msc) akan Muradun-ƙarni da ake yi musu laƙabi da ‘Sustainable Development Goals’ (SDGs) a Jami’ar Sussex da ke Brighton a Ƙasar Ingila.

Kuma yanzu na fara kararun Digirin-Digirgir (PhD) a ɓangaren ‘International Education and Development’ a School of Education and Social Work (ESW) da ke University of Sussex a Ingila.

Mu koma ɓangaren gwagwarmaya.

Daga cikin gwagwarmayar da na yi akwai ƙokƙari na buɗe gidauniyar Iya Hauwa (www.ihf.org.ng). Gidauniyar Iya Hauwa an yi mata ‘register’ da CAC/IT a shekarar 2016. Dalilin buɗe wannan gidauniya shine; ci gaba da tallafa wa al’ummarmu na karkara da ruga domin inganta da kyautata rayuwarsu a harkar lafiya, yaƙi da talauci, ilimin ‘ya’yansu da sauran duk abubuwa da suka shafi rayuwa waɗanda muradun-ƙarni (SDGs) ke ƙoƙarin ƙarfafawa.

Mu na ba wa ilimi muhimmanci ƙwarai da gaske a faɗakarwa da mu ke yi wa al’ummarmu, saboda ni na san daɗin ilimin tunda na fito daga Ruga, na samu na yi karatu har zuwa Ingila, kuma na samu dama masu yawa ta hanyar wannan ilimin da na ke da shi.

Ko Hajiya na yin wani aiki baya ga na hidimar jama’a?

Na yi ayyuka da dama daga koyarwa a aji, zuwa aiki da ƙungiyoyi na gida (a cikin ƙasarmu Nijeriya) da ƙungiyoyi na ƙasashen waje. Aikina na ƙarshe da na yi shine, mai taimaka wa gwamna a ɓangaren mata (Special Assistant on Women Empowerment), na yi aiki da mai girma Gwamna Alhaji Badaru Abubakar (MNI) Gwamnan Jihar Jigawa.

Za mu so mu ji irin ƙalubalai da kika fuskata a tafiyar rayuwa?

Ƙalubale na rayuwa da ake fuskanta bai wuce rashin kuɗi da rashin lokaci ba. Annobar Korona ta taimaka wajen matsalar rashin kuɗi, saboda duk abubuwa sun tsaya cak, mutane ɗai-ɗaiku da suke taimaka mana su ma abubuwan sun tsaya, haka kuma ƙungiyoyi masu tallafa wa ƙananan ƙungiyoyi su ma sun ɗan ja da baya, saboda wannan annoba ta Korona da aka sha fama da ita.

Abu na biyu shi ne, kamar yadda na faɗa, rashin lokaci, abubuwan da ke buqiatar a mayar da hankali domin aiwatar da su sai kaga a samu ƙarancin lokaci domin aiwatar da su ɗin, saboda abubuwa da su kayi mana yawa, kamar karatuna da kuma lura da iyali da kuma fafutuka wajen neman abinda za a biya buƙatun yau da kullum.

Na san ba za a rasa nasarorin da aka samu ta sanadiyyar wannan faɗi-tashi ba.

wasu daga cikin manyan nasarori da na samu a rayuwa akwai wannan ilimin da na faɗa a baya da kuma samun damar kafa gidauniyar Iya Hauwa (Iya Hauwa Foundation). A ɓangaren gidauniya mun samu nasarar farfaɗo da wata makaranta a wani ƙauye (Fajiganari) a Birniwa, sannan mun ɗauki masu koyar da su karatu musamman waɗanda suka kammala NCE, mu na ba su ɗan tallafi duk wata, ta dalilin wannan gidauniya mun samar da gina makarantun firamare guda biyu da famfon solar mai ɗaukar litar ruwa dubu goma a ƙauyuka biyar a Birniwa LGA wanda akwai Ruga da yawa a cikinsu. Mun samo waɗannan ayyukan daga ma’aikatar Gwamnatin Tarayya ta Ayyuka da Gidaje. (Federal Ministry of Works and Housing).

Hajiya Hauwa Umar Aliyu

Wane kira gare ki ga mata ‘yan’uwanki?

Gaskiya kira na ga ‘yan’uwana mata shine, a tashi tsaye a nemi ilimin addini da na boko Idan an samu hali. Ina kira ga matanmu na birni da na karkara a dage wajen koyon sana’o’i, mu dage mu nema wa kanmu ‘yanci ta haka ne za mu tsira daga ƙangin talauci. Mu nemi ƙungiyoyi da suke ayyuka waɗanda suka yi dai-dai da ra’ayinmu, mu shiga, kuma mu ba da tamu gudunmawar. Na ƙarshe kuwa, mata mu ne iyaye, lallai lallai mu kula da tarbiyyar ‘ya’yanmu.

Ko Hajiya ta je wasu ƙasashe don aiki ko buɗe ido?


Lallai na je wasu ƙasashe, amma ba su da yawa. Ƙasashen da na je su ne; Niger zumunci, sai karatu ya kai ni Ƙasar Kenya, na kuma samu damar sauke farali zuwa Ƙasar Saudiyya, haka kuma yawon buɗe ido ya kai ni Ƙasar Dubai da Faransa da kuma Belgium da Turkey, sannan na je Ƙasar Netherland ita ma buɗe ido, sai kuma aiki da ya kai ni Italy, sai Ƙasar Ingila karatu.

Wane kalar abinci kika fi so?

(Dariya). Abincin da na fi so shine tuwo da miya.

A ɓangaren tufafi wane ne zaɓinki?

kalar kayan da na fi so, kowacce iri Ina so, amma ɗinkin doguwar riga.

Mun gode.

Ni ma na gode. Allah ya ƙara ɗaukaka ku.