Matacce ya tashi ana daf da ƙona shi

Wani ɗan ƙasar Indiya ya tsallake rijiya da baya ana daf ƙona shi da ransa bayan yayin da ya farka ana tsaka da jana’izarsa ‘yan mintuna kafin ya banka wuta.

Hakan ya faru ne biyo bayan gazawar wani likita na yin gwajin tabbatar da mutuwarsa, inji jami’an kiwon lafiya a ranar Asabar, 23 ga watan Nuwamba.

Rohitash Kumar, ɗan shekara 25 mai fama da matsalar magana da ji, an kai shi wani asibiti a Jhunjhunu, Rajasthan, ranar Alhamis bayan ya yi fama da rashin lafiya.

Rahotanni sun nuna cewa ya sha fama da ciwon farfaɗiya. Sai dai wani likita ya bayyana cewa ya mutu da isar sa asibiti.