Matafiya sun fusata sakamakon tsadar tikitin jirgin ƙasar Kaduna zuwa Abuja

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A safiyar yau talata ne aka ga fasinjoji a tashar jiragen ƙasa na Kaduna da ke Rigasa sun harziƙa kan yadda wasu mutane da ake zargin ba ma’aikatan Hukumar Jirgin Ƙasar ba ne na saran tikiti tare da sayarwa da tsada har sama da naira dubu goma.

Wannan lamarin dai ya tilasta wa fasinjoji suka riqa sayen tikitin a kan farashin dubu goma wanda ya yi tsada ga talakawa a hannun ’yan kasuwar bayan-fage da ba a iya tantance ko su wane ne ba, kamar yadda wakilin Manhaja ya shaida.

Tun a watan Janairu ne hukumar Jiragen Ƙasa ta Ƙasa (NRC) ta mayar da sayen tikitin jirgin ƙasa na Kaduna zuwa Abuja ta yanar gizo maimakon layi na yanar gizo da ake bi a saya a tashar jirgin da ke Abuja da Kaduna.

Wata mata a wajen sayen tikitin, mai suna Rabi Salisu, ta shaida wa wakilin Manhaja cewa, “a ranar Juma’ar da ta gabata ne wani mutum a wajen sayen tikitin ya ce, ba zai sayar min da tikiti ba har sai na ba shi naira dubu ashirin da biyar, wanda da ƙyar na samu ya bar min a farashin naira dubu goma sha biyar daga ƙarshe.”

Manhaja ta shaida cewa, halin tsaron da ake ciki kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ne ya tilasta wa matafiya yin tururruwa zuwa tashar jirgin ƙasar domin tsira da ransu.

Fasinjojin na ƙoƙarin kauce wa masu garkuwa da mutane ne don neman kuɗin fansa a hanyar Kaduna zuwa Abuja, muddin suka bi hanyar mota.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *