Mataimakin Gwamnan Katsina ya ajiye muƙaminsa

Daga UMAR GARBA a Katsina

Mataimakin gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Mannir Yakubu ya ajiye muƙaminsa na kwamishinan ma’aikatar aikin gona, muƙamin da yake riƙe da shi tun kimanin shekaru 7 da su ka wuce a bisa jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari.

Mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Ibrahim Musa Kalla ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai jiya Alhamis.

Kalla ya bayyana cewar mataimakin gwamnan ya ajiye muƙamin nasa ne don bin umarnin sabuwar dokar zaɓe da shugaban ƙasa ya saka wa hannu mai lamba 84(12) ta shekarar 2022 wadda aka gyara.

Ya ƙara da cewa bayan tanadin dokar zaɓe, Mannir Yakubu ya ajiye muƙamin kwamishinan ne don ci gaba da shirye-shiryen ayyana takarar sa ta gwamnan Jihar Katsina wadda zai ayyana bada jimawa ba.

Mataimakin gwamnan ya gode wa Allah, daga nan sai ya gode wa Gwamna Aminu Masari bisa damar da aka ba shi don dawo da martabar aikin gona a jihar.

Daga ƙarshe Yakubu ya bayyana farin cikinsa bisa yadda aka haɓɓaka ɓangaren aikin noma a jihar duba da yadda manoma suka samar da abinci gami da samar wa masana’antun aikin gona kayan da suke buƙata a jihar Katsina dama ƙasar baki ɗaya.

Q.S Mannir Yakubu ya na ɗaya daga cikin mutanen da ke fatan ganin sun gaji kujerar gwamnan jihar Katsina a manyan zaɓukan dake tafe na shekara ta 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *