Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Kaduna ya sauya sheƙa daga APC zuwa LP

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Isaac Auta Zankai da wani ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazavar Zariya, Suleiman Dabo, sun fice daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar LP.

Sakataren Jam’iyyar LP na Ƙasa kuma Shugaban Majalisar Gwamnan Jihar, Umar Farouk Ibrahim ne ya bayyana hakan a yayin ƙaddamar da majalisar yaƙin neman zaɓen jam’iyyar mai wakilai 450 da kuma aaddamar da taronta a Kaduna ranar Alhamis.

Ibrahim ya ce, rabin ’yan majalisar dokokin jihar magoya bayan takarar Obi-Datti nd, inda ya ce goyon bayan da aka samu daga masu kishin jihar, alama ce da ke nuna cewa jam’iyyar na shirin karcar ragamar mulki a jihar, jihohi da na ƙasa a babban zaɓe mai zuwa.

Ya ce, “Gaskiyar magana, yau shine lokaci mafi farin ciki a rayuwata. Na zagaya domin yi wa ɗan takararmu na shugaban ƙasa, Peter Obi yaƙin neman zaɓe, kuma mun samu gagarumar tarba.

“Na yi matuƙar farin ciki sosai da irin rawar da suka taka a wannan bikin aaddamarwar. A duk faɗin jihohin Arewa ba mu da wani mutum da ya fice daga APC ya koma jam’iyyar LP sai a Jihar Kaduna tare da Mataimakin Shugaban Majalisar da kuma wani ɗan majalisar wakilai daga mazaɓar Zariya,” inji shi.