Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dattawa ya sauya sheƙa zuwa APC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sanata mai wakiltar Taraba ta Kudu kuma mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, Emmanuel Bwacha, ya sauya sheƙa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC). 

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya tarbi Bwacha zuwa APC a hukumance a Fadar Shugaban Ƙasa jiya Alhamis, inda ya miƙa masa tutar jam’iyyar mai mulki.

Shugaban Kwamitin Riƙon Ƙwarya na APC kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya gabatarwa Buhari da Bwacha a fadar Villa da ke Abuja. 

Mai ba shugaban ƙasa shawara a kan kafofin sadarwa ta zamani, Buhari Sallau ne ya sanar da batun sauya sheƙar sanatan a shafinsa na Tuwiter. 

“Shugaban riqon ƙwarya na APC kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da sabon mambar jam’iyyar, mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Emmanuel Bwacha, a yayin gabatar da sanatan wanda ya sauya sheka zuwa jam’iyyar daga PDP a baya-bayan nan a fadar shugaban ƙasa.” 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *