Mataimakiyar firaministan Sin ta buƙaci a ɗauki matakan daƙile cutar COVID-19 cikin ƙanƙanin lokaci

Daga CMG HAUSA

Mataimakiyar firaministan ƙasar Sin, Sun Chunlan, ta buƙaci yankunan dake fama da tsananin yaduwar annobar COVID-19 su yi ƙoƙarin daƙile cutar a cikin ƙanƙanin lokaci.

Sun, ta yi wannan tsokaci ne a wajen taron majalisar gudanarwar ƙasar ta wayar tarho game da matakan yaƙi da annobar COVID-19.

Sun ta ce, ya kamata a ƙara ƙoƙarin faɗaɗa ayyukan gwaje-gwajen cutar, da faɗaɗa ayyukan tantance yanayin lafiyar jama’a, da aikin jigilar marasa lafiyar da kuma aikin killacewa.

Ta ƙara da cewa, ya kamata a bayar da fifiko wajen kandagarkin hana shigo da cutar daga ƙetare, inda bangaren tashoshin ruwa zasu kasance a matsayin ginshiki.
Sun ta kuma bukaci makarantu da su ƙarfafa ayyukan binciken lafiya dake gudana a kullum, a ƙara yawan adadin gwajin cutar da ake gudanarwa, da kuma samar da matakan kariya daga fuskantar yaɗuwar cutar.

Babban yankin ƙasar Sin ya tabbatar da sabbin alƙaluman masu kamuwa da cutar COVID-19 kimanin 1,938 a ranar Asabar, daga cikinsu akwai mutane 1,807 da suka kamu da cutar a cikin gida, ragowar mutane 131 kuma suka shigo da cutar daga ƙasashen ƙetare, kamar yadda alƙaluman da hukumar lafiyar ƙasar ta bayyana a yau Lahadi.

Baya ga haka, kimanin sabbin mutane 1,455 aka samu sun kamu da cutar ba tare da nuna alamomin cutar ba, yayin da majinyata 6,287 ne ke ƙarƙashin kulawar likitoci waɗanda ba su nuna alamomin kamuwa da cutar ba.

Fassara: Ahmad