Matakan da gwamnati ke ɗauka kan tsaro ya taimaka wajen haɓaka kasuwancin kayan gwari – Shugaba

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Shugaban kasuwar kayan gwari ta ƙasa da ƙasa ta Mile 12 da ke Legas, Alh Shehu Usman Jibril, ya bayyana cewa matakan da gwamnati ke ɗauka na inganta lamurran tsaro a Nijeriya ya taimaka wa lamurran kasuwancin kayan gwari, musamman na iya safarar su daga jihohin Arewa dake fama da matsalar tasaro zuwa kasuwar kayan gwari ta Mile 12.

Shugaban ya bayyana hakan ne a wajen taron shekara-shekara da jagororin kasuwar ke gudanarwa a duk shekara domin tattauna nasarori da irin ƙalubalen da masu noma da kasuwancin kayan gwarin ke fuskanta, taron da a wannan shekarar ya gudana a jihar Sakkwato.

“Mun shirya wannan taron ne domin fahimtar juna, tsakanin masu noma da safarar kayan gwari da ma mu da ake kai wa kayan, dama yin nazari kan irin nasarori da ƙalubalen da sana’ar tamu ke fuskanta domin yin gyara, inda ke buƙatar gyaran, la’akari da irin ƙoƙari da kasuwar ke yi wajen samar da ayukkan yi ga dubban jama’a a jihar Legas,” inji shi.

Babban sakataren wanda hakama shine ya wakilci shugaban ƙungiyar na kasuwar Mile 12 dake Legas, ya ƙara da cewa sukan zauna su rubuta ƙorafe-ƙorafen da aka gabatar masu tare da komawa da su domin tattaunawa ta musamman a tsakanin shuwagabannin kasuwar ta Mile 12 domin yin duk mai yuwa wajen ɗinke wannan ƙorafin da ‘yan kasuwar suka gabatar masu.

Shugaban kasuwar wanda ya maganta a ta bakin sakataren kasuwar Alh Idris Balarabe ya ce sam matsalar tsaro ta daina shafuwar kasuwancin da suke gudanarwa, idan aka kwatanta da lokacin baya da matsalar ta mamaye kusan dukkanin jihohin da ake noma kayan gwarin a jihohin Arewa.

“Ka ga a Maiduguri an samu matsalar Boko Haram, matsalar da ta hana su yin noma da sauran kayayyaki irin busashen tattasai da kifi da ake kai wa duka abun ya tsaya saboda matsalar nan ta tsaro, to amma a baya-bayyanan an samu cigaba, idan kaduba a kasuwar Damasak za ka ga ana cin kasuwa, kuma kaga suna noma da sauran su, hakama arewa maso yamma gwamnonin na kokari ta bangaren tsaro, sukan nemi Gwamnatin Tarayya, ita kuma ta tura dakarun ta domin kai farmaki ga waɗannan ‘yan ta’addan.”

Bisa wannan ne shugaban yayi kira ga ‘yan kasuwa da su riƙa sanya tsoron Allah a dukkanin lamurran kasuwancin da suke gudanarwa.

Shi ma da yake magantawa shugaban ƙungiyar masu noma da kasuwancin albasa na ƙasa, Aliyu Mai Ta Samu Isa, wanda mataimakin sa Dr Mansur Muhammad Aleru, ya bayyana jin dadinsa kan zabar Sakkwato domin gudanar da taron, la’akari da irin muhimmancin da jihar Sokoto ke da wajen noma dama fiton kayan gwarin da ake samarwa.

Kamar yanda ‘yan kasuwar Mile 12 suka ɗauke mu da muhimmanci, muma haka muka dauke su da muhimmanci, kuma zamu cigaba da basu goyon bayan duk da suke buƙata domin samun nasarar kasuwancin namu a cewar shugaban.

Taron da ya cirato mahalartan sa da suka hadar manoma, ‘yan kasuwa, dama shuwagabannin rassan kayan gwarin, ya sanya Aliyu Muhammad Tsagau da ke zamowa shugaban manoma da kasuwancin Karas na jihar Sakkwato bayyana irin tarin nasarorin da suka sama duk kuwa da tarin ƙalubalen dake ci masu tuwo a ƙwarya.

“Ɗaya daga tarin nasarorin da muka samu shine, samun haɗin kan al’umma domin fahimtar abinda jagorori suka zowa manoma da masu kasuwancin albasar da shi.

Jihar Sakkwato dai na daga cikin jihohin da su ka yi fice a Nijeriya, wajen noma kayan gwari irin su Albasa, Karas, Latas, Kokumba, Tattasai, Tarugu, Yalo, Tumatir da sauran kayan gwarin amfanin yau da kullum.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *