Matakan da ma’abuta kwalliya za su bi don kare fatarsu

Daga AMINA YUSUF ALI

mata ma’abuta kwalliya yau filin na share hawayenku ne, domin abu ne sananne mata da yawa su na kukan matsalolin da suke gani tare da fatarsu musamman ma fuska, waɗanda suka kasa gano dalilin aukuwan su. Da yawa na bazama neman magani don kawar da matsalolin, sai dai abin takaice ko sun magance su na ɗan lokaci ne, sai su dawo. Hakan kan sa su shiga damuwa tare da halin tambayar kai.

Idan kina ɗaya daga cikin matan da ba sa rabo da yin kwalliya a kullum, ga wasu matakai da za ki dinga amfani da su domin ki kare lafiyar fatarki.

Wanke fuska kullum da daddare:
An san abu ne mai ɗan wuya a ce kullum ki wanke fuskarki da daddare kafin kwanciyar bacci. Amma domin kare lafiyar fatarki, ya kamata ki dimanci wannan ɗabi’a. Da farko za ki fara sa sinadarin goge kwalliya ki goge fuskarki sannan ki wanke ta.

Wanke burushin shafa kwalliya a kai- a kai:
Wannan ma zai yi wuya a ce ana gudanar da shi kullum. Amma za ki iya wanke su wata-wata. Yin hakan zai iya kare ki daga ƙwayoyin halitta masu cutarwa da suke maƙalewa a jikin burushin waɗanda suke samuwa daga gumi, matacciyar fata, wasu kuma daga kayan kwalliyar.

Ki nemi kayan kwalliyar da zai amshi fatarki:
Kowa da irin yanayin fatarsa. Don haka sai ki kula ta hanyar gwaji ki gano kayan kwalliyar da yake jawo illa ga fatarki. Da kuma wanda ya dace da ita. Wasu kayan za su iya busar miki da fatarki. Yayin da wasu kuma suke iya ƙara mata maiƙo. Amma da yawa likitocin fata sun fi raja’a a kan a yi amfani da kayan kwalliyar da aka yi daga sinadaran ƙasa domin sun fi rashin illa ga fatar mutum.

Yin amfani da mai mai maiƙo da sinadarin kare zafin rana:
Mutane da dama ba su ɗauki shafa mai mai maiƙo ko sinadaran kariya daga rana a matsayin abubuwan da ya kamata su zama a jerin kayan kwalliyarsu na kullum ba. Amma suna taimakawa wajen hana bushewar fata da kuma hana saurin tsufa. Ki guji yin kwalliya a kan fatar fuskar da ta zama busasshiya ko mai kaushi. Idan ma za ki yi, yi amfani da sinadarin kare rana da mai mai maiƙo. Yanzu ma an sauƙaƙa wa mutane, dukka su biyun sukan zo a tare cikin kwalaba guda.

Banda ba da aron kayan kwalliya:
A guji ba da aron kayan kwalliya ko da kuwa ba da aron jambaki ne ga ƙawarki. Kodayake ke za ki ga ba komai ba ne, amma ita ce hanya ma fi sauɗi ta yaɗa ƙwayoyin cuta. Kuma hakan zai illata fatarki a gaba.

Idan kika riqe waɗannan matakan kariya masu sauƙi, za su taimaka wa fatarki ta zama lafiyayya kuma mai ƙyalli. Ita kwalliya a karan-kanta ba ta da illa ga fata kawai sai dai wasu ɗabi’u da mutane suke yi, su suke sa a samu matsala a fata.

Waɗannan matakan da aka zano a sama, duk da sauƙinsu amma idan aka yi amfani da su, za su kiyaye fatarki daga abubuwan illata fuska kamar bar-ni -da-mugu, saurin tsufa, da kuma bushewa da maiƙon fuska.