Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar da ke Yaqi da Safarar Mutane a Nijeriya (NAPTIP) ta ce aƙalla mata da ‘yan mata ‘yan Nijeriya sama da 25,000 da aka yi safarar su ne suka maƙale a Mali.
Kwamandan hukumar mai lura da shiyyar Benin, Mista Nduka Nwanwenne ne ya bayyana hakan a ranar Talata a wani taron bita da aka shirya wa ƙwararru kan harkokin yaɗa labarai a birnin Legas.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya NAN ya ce an shirya taron bitar ne domin bunƙasa ƙwarewar mahalarta taron wajen wayar da kan jama’a kan illolin da ke tattare da safarar mutane.
Ita ma babbar daraktar hukumar ta NAPTIP, Fatima Waziri-Azi, ta ce babban maƙasudin taron bitar shi ne jawo hankalin ƙwararrun kafafen yaɗa labarai kan mummunar ɗabi’ar safarar mutane domin ƙara wayar da kan jama’a kan illolin.
Mista Nduka ya ce “Binciken da hukumar NAPTIP ta gudanar ya gano cewa ana yaudarar mafi yawa daga cikin matan ne da kuɗi wajen yin safararsu, domin kuwa a cewarsa binciken nasu ya gano cewa mazan Mali sun fi kashe wa mata kuɗi idan aka kwatanta da na Nijeriya.
Kwamandan ya ce hukumar ta kama mutum 9,102 da ake zargi da safarar mutane, tare da kuɓutar da mutum 20,660 tsakanin 2004 zuwa Mayu 2023.