Matar Alaafin na Oyo ta bi shi bayan makwanni kaɗan da rasuwarsa

Daga AMINA YUSUF ALI

Makwanni kaɗan da rasuwar Sarkin Oyo wanda aka fi sani da Alafin ɗin Oyo, Oba Lamidi Adeyemi III, ɗaya daga cikin matansa mai suna Olori Kafayat, ita ma ta ce ga garinku.

Rahotanni sun bayyana cewa, basarakiyar mai suna, Olori Kafayat, wacce mahaifiya ce a gurin ɗan sarkin wato, Yarima Adebayo Adeyemi, wanda aka fi sani da D’Guv, ta rasu ne ranar Juma’a 1 ga Yuli, 2022.

Cikakken bayani a game da mutuwar tata dai bai samu ba. Har lokacin da aka haɗa wannan rahoton dai babu wani ƙarin bayani. Amma daraktan kafofin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na fadar Alafin ɗin Mista Bode Durojaye, ya tabbatar wa da manema labarai zancen mutuwar Tata a safiyar ranar Asabar, 2 ga Yuli, 2022. Kuma ya bayyana cewa, ta rasu ne a ƙasar Amurka.

Olori Kafayat Adeyemi, dai an ce ita ce mata ta huɗu daga jerin matan Alafin, Oba Adeyemi III. Sunan da ta yi fice da shi kuwa shi ne sunanta na sarauta wato, Iya Aguo ko Iya Ibeji ta masarautar Oyo.

Shi dai Sarkin Oyo, Oba Adeyemi III ya rasu ne ranar Juma’a 22 ga watan Afrilu shekarar 2022. Ya rasu ne a asibitin koyarwa na Jami’ar Afe Babalola dake garin Ado Ekiti, bayan ‘yar gajeriyar jinya. Ya rasu yana da shekaru 83 a Duniya.

Tun bayan dai rasuwar Oba Adeyemi, har yanzu ba a samu wani sabon Alafin ɗin da ya ɗare kan gadonsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *