Matar da aka sace a harin jirgin ƙasa ta haihu a hannun ‘yan bindiga

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ɗaya daga cikin fasinjojin da ‘yan fashin daji suka sace daga jirgin ƙasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna ranar 28 ga watan Maris ta haihu a hannun masu garkuwa da ita.
Tashar talabijin ta AriseTV, wadda ta wallafa wannan labarin, ta kuma ce wani ɗan uwan matar ne ya sanar da su haka.

Ɗan uwa nata ya sanar cewa an kai wani likita wurin da ake riƙe da ita wanda ya taimaka mata wajen haihuwa.

“Matar na da tsohon ciki wanda ya kai wata takwas yayin da aka sace ta da sauran gwamman fasinjoji, kuma ta haihu ne bayan da ‘yan ta’addan suka gayyaci likitoci su karɓi haihuwar. Sai dai ba mu san halin da abin da ta haifa yake ba,” in ji ɗan uwan matar.

A farkon wannan makon ne dai masu garkuwa da mutanen suka wallafa hotunan fasinjojin da kawo yanzu suka shafe wata guda cur a hannunsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *