Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Matar da ta kafa Kasuwar ‘Mammy Market’ a barikin sojoji a faɗin ƙasar nan, Maria Ochefu, ta mutu.
Dan ta, Farfesa Yakubu Ochefu, wanda ya zanta da wakilin Punch ta wayar tarho a jiya Alhamis, ya ce ta mutu ne a cikin barcin da take yi a ranar Talata.
Mai shekaru 86, ta auri Kanar Anthony Ochefu, wanda ya taɓa zama gwamnan soji a jihar Enugu.
A wata hira ta ƙarshe da ta yi da jaridar Punch a shekarun baya, Ochefu ta bayyana yadda ta fara Kasuwar Mammy, wadda daga baya ta zama hantsi leƙa gidan kowa a duk barikin sojoji da ke faɗin ƙasar nan.
A yayin tattaunawar, ta ambaci wasu shugabannin ƙasa guda biyu da suka shuɗe, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya) da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, duk sun yi ritaya a matsayin kwastomominta.
Ochefu ya ce, “Eh, Mama ta rasu ranar Talata a Makurdi tana tsaka da barci,” inji ɗan nata.