Matar El-Rufai ga ‘yan Nijeriya: Ku shirya sadaukar da ranku don kawo ƙarshen matsalar garkuwa da mutane

Daga AISHA ASAS

Matar gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Asia el-Rufai, ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da su shirya sadaukar da rayuwarsu domin kawo ƙarshen harkokin ‘yan fashin daji da garkuwa da mutane.

Asia ta bada misalin cewa idan ya zamana an yi garkuwa da ita, a shirye take ta rasa ranta muddin hakan shi zai kawo ƙarshen bala’in.

Matar gwamnan ta yi waɗannan bayanan ne sa’ilin da take jawabi a wajen wani taron horar da ‘yan’uwanta mata kan sha’anin zaman lafiya da tsaro wanda cibiyar Equal Access International (EAI) ta shirya a Larabar da ta gabata a Kaduna.

Daraktan EAI a Nijeriya, Maaji Peters, ya ce an shirya horaswar ne domin tabbatar da tsaro a garuruwan Nijeriya ta hanyar ƙirƙiro da Shirin Tsaron Farar-hula (Civilian Security – CIVSEC) wanda zai bada gudunmawa wajen daƙile matsalolin da ke addabar al’umma.

Da take magana kan batun rikicin ƙabilanci da ake samu a wasu sassan Kaduna, Asia ta shaida wa matan da su guji dukkanin bayanan son-kai na ‘yan siyasa waɗanda ka iya lalata haɗin kan ‘yan jihar.

Matan da taron ya shafa an zaɓo su ne daga ƙananan hukumomin Chikun da Kajuru da kuma Jama’a.

A matsayinta na babbar baƙuwa a wajen taron, Hajiya Asia ta ce wajibi ne ga ‘yan Nijeriya su dawo da haɗin kan nan da aka san su da shi a baya wanda kuma mata na da rawar da za su taka wajen cimma hakan.

Tare da cewa: “Dole ne mu yi sadaukarwa don kawo ƙarshen wannan matsala. A shirye nake da in rasa raina a hannun masu garkuwa da mutane muddin hakan zai haifar da zaman lafiya a ƙasa.

“Idan kuka ci gaba da biyan kuɗin fansa, daidai yake da kamar kuna ƙara zuba wa wuta kananzir ne, kuna bai wa ‘yan fashi kuɗaɗe suna mallakar makaman da za su ci gaba da farautar ku da su. Mu daina biyan fansa. Wannan shi ne ra’ayina.

“Na faɗa a baya yanzu ma zan sake faɗi, idan aka yi garkuwa da ni ko ƙwandala kada ku biya fansa. Maimakon haka, ku yi mini addu’ar idan mutuwa ce, in tafi cikin salama in kuwa za a sake ni kada ya zamana an cutar da ni.”

Kazalika, ta ce “Muddin ba mu haɗu mun dakatar da wannan matsalar ba, za su gama da mu baki ɗaya. Har ma da mai kai kuɗin fansar ba za su ƙyale ba. Ai kuna ganin yadda wasunsu bayan an biya fansa duk da haka ba su ƙyale mutum, kun ga wannan ya zama hasara biyu kenan.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *