Matar hamshaƙin ɗankasuwa, Aminu Ɗantata ta riga mu gidan gaskiya

Hamshaƙin ɗan kasuwar nan na garin Kano, wato Alhaji Aminu Ɗantata, ya yi rashin matarsa Hajiya Rabi Aminu Ɗantata wadda aka fi sani da Mama Rabi.

Majiyar jaridar News Point Nigeria ta ce, a ranar Asabar Allah Ya yi wa marigayiyar cikawa a wani asibitin ƙasar Saudiyya bayan fama da rashin lafiya.

Mama Rabi, wadda ta kasance mata ta biyu ga Aminu Ɗantata, ta bar duniya tana da shekara 70 da ɗoriya.

Kuma ta rasu ta bar mijinta da ‘ya’ya shida da suka haɗa da Tajjuddeen Ɗantata, Batulu Ɗantata, Hafsa Ɗantata, Jamila Ɗantata da kuma Aliya Ɗantata.

Kazalika, ta bar jikoki da daman gaske.