Assalam alaikum. Babban abin da ke addabar matasa maza da mata shi ne, sha’awa. Kusan kullum matasa na faɗawa cikin bala’in fasiƙanci kala-kala a dalilin rashin sanin hanyar kaucewa haka.
Idan mutum ya yi duba na tsanaki tare da la’akari da yanayinmu da kuma yanayin zamani da muke ciki zai ga cewar da yawa wasu na faɗawa cikin aikata fasiƙanci ba cikin son ransu ba, sai don abin ya fi ƙarfinsu.
Sau da yawa za ka ga matashi mai hankali mai tarbiyya mai tsoron Allah, ya san illar zina, ya san girman zunubinta, amma saboda fitinar sha’awa ya ka sa daurewa har sai ya je ya aikata ɗin. Wani haka zai ta aikatawa yana tuba da haka har zina ta zame masa jiki ya run ka ganin ai yinta ba komai bane.
Haka za ka ga yarinya kamila mai tarbiyya mai hankali, ta san illar zina, ta san girman zunubinta amma sai fitinar sha’awa ta sa ta afka cikin wannan bala’i.
Domin kaucewa faɗawa makaranatar Shaiɗan, dole ne duk wani matashi da yake fuskantar barazanar sha’awa ya yi la’akari da wasu dokoki da addini ya shar’anta masa, sannan kuma ya yi amfani da dabaru wanda za su taimaka masa.
Mu sani cewa fitinar sha’awa halittace kuma a zuciya ta ke, daga cikinta ta ke bijirowa, don haka mai son ya iya danne fitinar sha’awarsa duk lokacin da ta taso masa, sai ya fara da gyara zuciyarsa tukunna.
Ana gyara ta ne ta hanyar cikata da kyawawan tunani da yanke duk wata igiyar mummunan tunani daga cikin ta da goge mazaunin duk wani mummunan shauƙi. Daga nan sai kyautata ɗabi’u da halaye da ayyuka, duk wata ɗabi’ar wani hali ko wani aiki da mutum ke yi indai bamai kyau ba ne, to yin watsi da shi zai qara haskaka masa zuciyarsa.
Kyawawan ɗabi’u sun haɗa da yawan murmushi, taimakawa ‘yan’uwa, makwabta da abokai, gaskiya da riƙon amana da sauransu. Kyawawan ayyuka sun haɗa da taka tsan-tsan wajen tsaida addini, duk abin da aka sa ba daidai ba ne a addinance sai a yi ƙoƙari a barshi komai daɗinsa ko ribarsa.
Yawan sanya Allah a zuciya da yin zikiri. Kiyaye ibada yana daga cikin maganin da yake wa mutum kandagarki daga fitinar sha’awa.
Lallai ne ’yan’uwa mu kula da kiyaye sallolin farilla da nafila da yawaita karatun Alƙur’ani da sauran azkar.
Haka kuma dole su kansu iyaye su kula da rayuwar ‘ya’yansu matasa maza da mata, domin kare su daga wannan bala’i.
Daga Ahmad Musa. 07041094323.