Matasa na da rawar takawa wajen bunƙasa harkar kasuwanci a Kano – Abdul Aja

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An bayyana cewa matasa suna da rawar da za su taka wajen cigaba da bunƙasa harkar kasuwanci a Jihar Kano.

Alhaji Abdu Muhammad Aja, ɗaya daga cikin iyayen kasuwar Wapa ne ya bayyana hakan a lokacin da ake rantsarda sabbin zaɓaɓɓun ƙungiyar ‘yan canji ta Al’amanat ta Wapa.

Ya ce abin farin ciki shine sabon zaɓaɓɓen shugaban qungiyar Alhaji Sani Salisu Dada tun yana zagayen yaƙin zave ya ce yana neman taimakonsu a matsayinsu na iyayen ƙungiya da yayyen sa da sauran tsofaffin shugabanni.

Ya fara da cewa in Allah ya so ya yarda zai cimma nasara tunda har ya ƙuduri niyyar za a ba shi shawara kan ina aka dosa, ya za a yi, yadda za a yi. In Allah ya so su za su bada shawarar kirki.

Ya yi nuni da cewa suna kyautata zato ga sabon shugaban ƙungiyar zai iya riqeta, saboda yaro ne mai hankali ya yi harkoki da yawa da aiki ƙarƙashin mutane da dama kuma ya ƙare an rabu lafiya.

Alhaji Muhammad Aja ya ce a tarihin kasuwar Wapa an samu cigaba sosai duk da ‘yan matsaloli da ake fuskanta domin ita ce kasuwar da ta haifar da dukkan kasuwannin canji a Nijeriya. Domin a baya ma, in kaje Ingila za ka ga sunan Wapa.

Ya ƙara da cewa duk wanda yake canji a Nijeriya da kasuwar Wapa yake tutiya tun kafin a fito da harkar BDC da Babangida ya qirqiro dama ana canji a Wapa, saboda su sun taso ne sun gaje ta daga iyaye da kakanni.

Ya ce bunƙasar Wapa ta sa duk wani mai canjin kuɗaɗe in an wayi gari sai ya bugo waya ya tambaya ya ya ake ciki a harkar hada-hada ta canjin kuɗi. Sannan Wapa ce ta haifar da babbar ƙungiyar ‘yan canji ta ƙasa wadda suna da mambobi ‘yan Wapa daga cikin masu tafiyar da ita irinsu Almustapha Ƙofar Mata, Lawan Umar duk jiga-jigai ne a cikinta wadda Faruq Sulaiman shine ya fara riƙe shugabancinta ta ƙasa, yanzu kuma Aminu Gwadabe ne yake.

Alhaji Abdu Muhammad Aja ya yi kira ga ‘yan kasuwar su bai wa sabbin zaɓaɓɓun shugabannin ƙungiyar ta Al’amanat goyon baya don cimma nasara.