Matasa na yunƙurin hana zaɓe a Sakkwato

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wasu gungun matasa na yunƙurin tada fitina yayin da ake shirin soma zaɓen gwamna da na ’yan majalisar dokoki a Jihar Sakkwato.

Ma’aikatan zaɓe sun kwashe kayansu a rumfar zaɓe mai lamba 027 ta Aliyu Kyari kan hatsaniyar da matasa suka tayar suna masu cewar ba su yarda da a yi zaɓen ba.

Tun da sanyin safiyar wannan Asabar ɗin dai matasa maza da mata suka fara shiga layi yayin da ma’aikatan zaɓen suka hallara, sai dai kuma gudanar da zaɓen ya gagara a rumfar inda a ƙarshe aka kwashe kayan zaɓe.

Daya daga cikin ma’aikatan zaɓen, Ibrahim Yakubu, ya ce babu tsaro a rumfar don haka ba za su yi zabe ba ganin yadda matasa suke ta rigima a rumfar.

A cewar Yakubu, “dole mu dakatar da zaɓen duk ba mu fara ba saboda babu yadda za a yi mu fara aiki ana hatsaniya.”

Muhammad Bashar, wani matashi mai shekara 25 ya ce, “haka kawai wasu matasa suka zo suka tayar da rigimar cewa ba za a yi zaɓe ba.

“Yanzu burinsu ya cika don gashi an watse.”

Matashin ya ce rumfar tana da masu jefa ƙuri’a 500, “amma yanzu an yi hasarar ƙuri’unsu daga wasu marasa kishin ƙasa.”