Matasa ya kamata su jagoranci Nijeriya kasancewarsu ƙashin bayan al’umma – Abba Sa’ad

Daga ABUBAKAR M. TAHIR a Haɗeja

Haƙiƙa ya zama wajibi mutane su dawo hayyacinsu su gwada bai wa matasa ƙuri’un su, domin samar da ci gaba ga al’umma.

Abba Bin Sa’ad Haɗeja shi ne ya yi wannan kira a lolacin da yake tattaunawa da wakilin Manhaja a Haɗeja, inda ya bayyana cewa ya kamata matasa su zama jagororin ƙasar nan domin samun ci gaba mai ma’ana.

“Musamman idan ka duba halin ƙunci da ake ciki a wannan ƙasa, ga kuma halin rashin tsaro wanda duk wani ɗan Nijeriya babba da yaro ya san da wannan matsala.

Kamata a ce matasa su dage wajen ganin sun shigo tafiyar domin canja waɗannan yanayi da aka tsinci kai a ciki. Misali gwamnatin yanzu ta yi wa ‘yan qasa alƙawarin samar musu da tsaro amma ta kasa.

Saboda haka dole ne matasan mu su zo su sadaukar da lokacin su, kowace al’umma da matasanta take tinƙaho a matsayin wanda za su kawo musu caji mai ɗorewa.”

Sa’ad ya ƙara da cewa “kada mu dogara ga siyasa a matsayin hanyar rayuwar mu, gaskiya dole matashi ya tashi ya nemi na kansa. Ba zai zama komai sai an maka a gidanku ba, kai ma ka yi ƙoƙari ka zama mai tallafa wa ƙannenka da mahaifanka.”

Abba Bin Sa’ad ya ƙarƙare da yin kira ga gwamnatin Nijeriya, inda yake cewa a gaskiya gwamnatin nan ta yi wa talakawa alƙawuran wajen samar musu da ingantacciyar rayuwa, amma ba ta cika ba.

“To ka ga ya kamata a ce yanzu tsawon shekarun da ta ɗauka ya kamata ta cika wa talaka alƙawarin da ta ɗauka masa.

Rayuwa ta yi tsanani, talakawa suna cikin wani yanayi da suke buƙatar a tallafa musu, abinci ya yi ɗan karen tsada, ta’addanci da garkuwa da mutane sai ƙara ta’azzara suke. Ya kamata gwamnati ta san abin yi.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *