Matasan Arewa sun goyi bayan Tinubu kan ƙudirin sake fasalin haraji

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar tuntuɓa ta matasan Arewa, PNYF, ta yaba wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa ƙin amincewa da shawarar Majalisar Tattalin Arzikin ƙasa, NEC, na dakatar da sabon ƙudirin gyara haraji.

Idan za a iya tunawa, a taronta na 144 da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya jagoranta, majalisar ta buƙaci a janye ƙudirin, bayan wani taron gwamnonin jihohin arewa 19 da suka yi tare da wasu manyan shugabannin gargajiya na yankin da suka yi adawa da dokar sake fasalin harajin Nijeriya baki ɗaya.

Amma Tinubu, ta wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, ya buƙaci hukumar harajin ƙasar da ta bar ƙudurin ya ci gaba da gudana.

Sai dai ƙungiyar ta PNYF a cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun babban sakataren ta, Abdulkadir Bala, ta bayyana goyon bayanta ga matakin da shugaban ƙasar ya ɗauka na yin watsi da matsayin majalisar tattalin arziki, musamman ƙungiyar gwamnonin Arewa.

Bala ya jaddada cewa matsayar da ƙungiyar gwamnonin Arewa ta ɗauka bai dace da ra’ayoyin al’ummar yankin ba dangane da batun sake fasalin haraji.

“ƙungiyar Tuntuɓa ta Matasan Arewa (PNYF) ta yaba wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa ƙin amincewa da shawarar da Majalisar Tattalin Arziki ta ƙasa (NEC) ta bayar na janye ƙudirin gyara haraji,” in ji sanarwar.

“Muna kuma so mu fayyace cewa Arewa ba ta goyon bayan matsayar ƙungiyar gwamnonin Arewa dangane da batun sake fasalin haraji. Kiran da dandalin ya yi na a janye waɗannan ƙudirori ba ya wakiltar ra’ayoyin al’ummar yankin.

“Gwamnonin sun ci gaba da nuna gazawarsu wajen jagorancin Arewa, maimakon haka sun dogara da kason tarayya, suna almubazzaranci da dukiyar al’umma, maimakon gabatar da irin wannan ƙudiri don inganta kuɗaɗen shiga na cikin gida na jihohinsu, gwamnonin suna adawa da yunƙurin rage dogaro ga gwamnatin tarayya ba tare da fayyace ba.

“Idan da gaske gwamnonin suna son kula da mutanen yankunan su, da sun yi amfani da damar da suka samu wajen ba da shawarwari da kuma kawo sauye-sauye a lokacin aikin majalisar tattalin arziki, maimakon kira da a janye ƙudirin daga majalisar tarayya.

“Me ƙungiyar gwamnonin Arewa ke tsoro? A bayyane yake, suna tsoron ɗaukar alhaki. Suna son a ci gaba da samun tallafin kuɗi daga Gwamnatin Tarayya ba tare da yin wani yunƙuri na bunƙasa ayyukansu na samar da kuɗaɗen shiga ba. Babu wata shaida da ta nuna cewa gwamnonin Arewa na yanzu sun yi amfani da duk kason da suka samu daga gwamnatin tarayya ta Shugaba Tinubu.

“Ya kamata gwamnoni su daina adawa da ƙudirin doka da gwamnatin tarayya ta kawo su mayar da hankali wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu a kan jama’a. Idan ba haka ba, mutane na iya jin cewa dole ne su nemi a tsige su ko kuma su yi murabus.

“Har ila yau, muna yaba wa Shugaba Tinubu kan yadda ya jajirce wajen goyon bayan ƙudirin gyara haraji, duk da ƙoƙarin da wasu masu son kai suka yi na hana shi.

“Arewa na goyon bayan ƙudirin sake fasalin haraji, domin suna da nufin daidaita tsarin tafiyar da harajin Nijeriya, da gyara harkokin harajin kasarasar gaba ɗaya, tare da daidaita su da ingantattun hanyoyin daidai da na sauran ƙasashen duniya.”