Matasan marubuta ba sa son ana musu gyara – Mukhtar Ƙwalisa

A rubutu na yi aure, na yi muhalli na kaina”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Ga duk wani tsohon makarancin littattafan Hausa, musamman littattafan labaran yaƙe-yaƙe da na barkwanci ba zai kasa sanin littattafan marubuci Mukhtar Ƙwalisa ba, wanda ya yi suna wajen tsara labarai masu ɗaukar hankali da sanya nishaɗi a zuciyar mai karatu. A wannan makon, shafin Adabi ya gayyato muku ɗan ƙwalisar marubuta, don jin abin da ya sa har yanzu yake ci gaba da wallafa littattafai duk kuwa da kasancewar takwarorinsa da dama yanzu harkar ta gagare su. A tattaunawar da suka yi da wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, ne yake nuna shi da rubutu sun yi auren zobe ba rabuwa, don haka a shirye yake duk canjin da zamani ya kawo a harkar rubutu ya runguma. Ga Ƙwalisa nan ga Abba, a sha karatu lafiya.

MANHAJA: Zan so mu fara da jin ko wanene Mukhtar Ƙwalisa?

Ƙwalisa: To, Alhamdulillahi. Mukhtar Ƙwalisa dai matashi ne, marubuci, ɗan kasuwa, kuma mawallafi, daga Jihar Kano. Asalin sunana Mukhtar Isa Adamu, inkiyata ce Ƙwalisa. Na yi harkokin kasuwanci kala-kala daga ƙarshe dai na koma fagen rubutu inda abincina yake. Daga marubuci na zama mawallafi, ina bugawa mutane littattafansu, wato Publisher. Ina kuma da aure da yara biyu.

Ba mu taƙaitaccen tarihin rayuwarka.

An haife ni a Unguwar Briged, a nan bakin Sabuwar Kasuwa. Gidanmu yana nan a daidai da filin bal wato Mini Stadium, da ke Ƙaramar Hukumar Nassarawa a nan Jihar Kano. Shekaruna ba masu yawa ne sosai ba, don ba su haura 37 ba, Na soma karatuna a makarantar firamare da ke nan Briged, inda na kammala a shekarar 1998. Daga nan na wuce zuwa sakandire ta commercial da ke titin filin jirgin sama, inda na kammala a shekarar 2004. Sai kuma na samu damar shiga Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano wacce ake kira da CAS, na samu zarafin yin diploma, kuma na kammala a shekarar 2010.

A ina laƙabin Ƙwalisa na cikin sunanka ya samo asali?

E, gaskiya ana yawan tambayata a game da inda na samo wannan laƙabin. Na samu sunan Ƙwalisa ne daga bakin wani dattijo wanda muke kai wa guga yana yi mana, yadda ya fahimci ina son tsafta sosai da kwalliya shi ya sa yake kirana da Ƙwalisa. Ma’anar kalmar dai shi ne, mutum mai yawan son kwaliya. To, sannu bata hana zuwa sai sunan ya shiga bakin abokaina, a hankali kuma da yake a lokacin ina harkar ƙwallo sosai, sai sunan ya bini wajen bal, daga nan kuma ya zama inkiyata. Kusan kowa da wannan sunan ya sanni, don har ma ya rufe ainihin sunana. Idan ba Ƙwalisa ka ce ba to, bama a gane wa ka ke magana a kansa.

Tun yaushe ka fara jin sha’awar zama marubuci, kuma ta yaya ka fara?

Na soma sha’awar rubutu tun muna aji ɗaya na ƙaramar sakandire, wato JSS 1. Na fara rubuta wani littafi da na sa wa suna ‘Kasada’, da yake a lokacin ana yayin labari na ban tsoro. To, shi ma haka yake. Daga nan na cigaba da rubuta labarai, ina karantawa ‘yan aji idan ba malami. A haka har na fitar da littafina na farko mai suna ‘Guguwar So’, a shekarar da muka kammala Sakandire, wato 2004.

An sanka da salon rubutun labaran yaƙe-yaƙe, menene ya ja ra’ayinka har ka ɗauki wannan salon?

Rubutun yaƙi daga baya na soma shi. Na kuma soma shi ne domin neman kuɗi ba domin neman suna ba, saboda ko a lokacin na samu suna a harkar rubutu, domin na fitar da littattafan soyayya da zamantakewa kusan guda biyar. Tunda a lokacin na tsunduma a kasuwar littafi, sai na ɗauki rubutu a matsayin sana’a.

Don haka sai na kama rubuta littattafan labaran yaƙi, wanda a lokacin babu marubutan shi sosai, waɗanda ba su fi shida ba, kuma akwai makaranta labaran yaƙin sosai. Dalilin da ya sa kenan na karkata ga rubutu da wannan salon, tunda shi rubutu ne wanda ba shi da wahala sosai ba kamar na soyayya ba.

Kawo yanzu ka shafe shekaru nawa kana rubuce-rubuce?

Idan aka ɗauka daga shekarar 2004 da na bayyana a duniyar marubuta, da littafina mai suna ‘Guguwar So’ zuwa yanzu da muke shekarar 2023, na shafe shekaru aƙalla shekara 19, kuma a tsawon waɗannan shekaru na rubuta littattafai aƙalla 24, waɗanda suka fita kasuwa. Har yanzu kuma ina kan cigaba da rubutu, ban san kuma ranar dainawa ba.

Kawo mana sunayen littattafan da ka yi da bitar uku da suka fi fitar da sunanka a duniyar marubuta?

To, a ɓangaren littattafan soyayya na rubuta littattafai goma, da suka haɗa da ‘Guguwar So’, ‘Murmushin ‘Yan Mata’, ‘Kisan Aure’, ‘Ki Yi Haƙuri’, ‘Gidan Bilkisu’, ‘Wacece Mace?’ ‘Rai Da So’, ‘Yar Soyayya’, ‘Addini Akida’, da kuma ‘Duniyar Ma’aurata’.
A ɓangaren littattafan yaƙi kuma ina da littattafai takwas da na rubuta, da suka haɗpa da ‘Gimbiya Zahra’, ‘Ɗimauta’, ‘Addinina’, ‘Ranar Gamo’, ‘Gamo da Ajali’, ‘Ranar Mutuwa’, ‘Kitabul Maut’, da kuma labarin, ‘Yar Sarki’. Na kuma rubuta littattafan barkwanci har guda huɗu su ne, ‘Salon Nishaɗi’, ‘Jigon Nishaɗi’, ‘Salon Dariya’, ‘Gwanin Ban Dariya’.

Har wa yau kuma na rubuta wasu littattafan tatsuniya na yara guda biyu, da suka haɗa da ‘Tatsuniyoyin Gizo da Ƙoƙi’ na 1, na 2 da na 3, sai kuma littafin ‘Gidan Zoo’ na 1 & 2.

Daga cikin littattafaina da suka fi shahara akwai littafin ‘Wacece Mace?’ Labari ne na wata yarinya da ta bi maganar mahaifinta ta auri wani wanda ba ta son shi. Sai dai shi wanda ta auran ya kasance wani irin mutum ne wanda bai san darajar mace ba, ya ɗauki mace ne kawai a matsayin abin jin daɗi da kawar da sha’awarsa.

Don haka ya shiga ƙuntatawa rayuwarta, ya azabtar da ita, ya ƙara tsanarta. A lokacin da ta samu ciki ya ce a zubar shi ba ya son haihuwa a yanzu, ita kuma ta bijirewa umarninsa, shi kuma ya hanata zuwa awo da fita ko’ina. Haka dai labarin ya ci gaba har zuwa ƙarshe inda abinda ya faru, ya faru.

Sannan akwai littafina mai suna ‘Addina’, wanda labari ne na yaƙi, amma yadda aka zuba ilimi na addini da bincike na tarihi a ciki ya sa ya zama zakaran gwajin dafi a lokacin da ya fita.

Shi kuma littafin ‘RAI da So’ wani irin labari ne da na shafe shekara huɗu ina rubutawa da gyare-gyare, sannan na bai wa wasu ‘yan uwa marubuta da masu nazari suka duba labarin, kafin aka sake shi a kasuwa. Cikin sa’a kuwa bai jima da fita ba wani shehun malami a wata Jami’a ya ɗauke shi a cikin littattafai 30 da aka kai masa, don ya sakawa dalibai shi.

Labari ne da ya shafi camfe-camfe na Hausawa, inda aka gina labarin a kan wata budurwa wacce ta yi aure har uku, kuma duk wanda ta aura sai ya talauce ya tsiyace ya koma kamar beran masallaci. Littafina na ‘Tatsuniyoyin ‘Gizo da Ƙoƙi’ shi ma ya samu shiga cikin jerin littattafan da ake koyawa yara a wasu makarantu da ke nan Kano.

Wanne alheri za ka iya cewa ka samu a dalilin rubutu wanda ba za ka manta da shi ba?

Daga alheran da na samu a wannan harka ta rubutu zan iya cewa a ciki na yi aure na kuma yi muhalli nawa na kaina. Sai kyautar turare da wata makaranciya ta tava bani tun wajen 2007.

Haka nan an taɓa bani wata rigar mata, wacce kuɗinta ya kai kusan Naira dubu 50, wacce na bai wa iyalina. Na gamu da mutanen kirki, ‘yan’uwa marubuta masu son zumunci da nuna ƙaunar juna.

Gaya mana wanne ƙalubale ka tava samu a dalilin rubutu, wanda ya fi tsaya maka a rai?

Ƙalubalen da na fuskanta shi ne na bayyanar wani ɗan daudu daga Katsina, wanda shi kuma ya yi amfani da damar da kasuwar littafi ta shiga na karyewa, tun daga wata gobara da aka yi a kasuwar Sabon Gari, daga wannan lokacin sai Allah ya jarrabce mu da shiga wani yanayi, duba da maqudan kuɗaɗen da aka rasa na kayayyakin mutane.

Sai kuma harka a kasuwa ta soma taɓarɓarewa. Haka nan na samu kaina cikin jarrabawar tattalin arziƙi, wanda wannan damar da ita shi wancan ɗan daudu ya yi amfani bayan mun yi masa inuwa ya so ya fitar da ni tsakiyar rana, amma Allah bai so hakan ba. A taƙaice dai wannan shi ne babban ƙalubalen da na fuskanta. Sai ƙalubale na biyu, wanda kuɗaɗena da suke hannun wasu ‘yan kasuwa wasu a Kano, wasu Katsina, wasu Sakkwato, ga shi nan dai suna da yawa sosai.

Wasu daga cikin abokan tafiyarka a harkar rubutu da dama sun ajiye alƙalaminsu, kai me ya sa har yanzu ba ka haƙura ka daina ba?

A gaskiya ni dai ban sa ranar ajiye alƙalami ba, saboda ni ban gwanance wajen komai ba sai rubutu. Wataƙila nan gaba idan na samu wani aikin ko da na gwamnati ne. Su ma sauran da suka ajiye ka ga wasu ayyukan suka samu wanda suka saka dole suka haƙura da harkar rubutu, saboda sabgogi sun musu yawa.

Canjin zamani da ƙalubalen kasuwancin littattafai ya jawo marubuta sun koma fitar da littattafai a onlayin. Kai me ya sa har yanzu ka ke wallafa naka a takarda?

Har yanzu akwai makaranta da babu ruwan su da onlayin kawai sun fi ganewa karatu a takarda. Haka nan kuma na faɗa maka akwai littafi irin na yara kamar tatsuniyoyin gizo da ƙoƙi da na yi su, yara babu abinda ya shafe su da onlayin don haka ka ga har ya zuwa yanzu muna nan a duniyar takarda. Amma hakan ba yana nufin ba na tafiya da zamani ba ne.

Ni ma ina kai nawa littattafan a onlayin ɗin, da duk wata hanyar da ake bi wajen ganin ana siyar da littattafai.

Yaya ka ke iya mayar da abin da ka ke kashewa a talifi, da yadda ka ke isa ga masoya littattafanka?

Shi littafi na yanzu da muke yi muna yin sa ne kai-tsaye, wanda aiki ne mai wahala da kuma son nutsuwa sosai a lokacin da ka ke yin sa, domin ana yin sa ne da abin gurza takarda na printer. Wannan damar ta bamu zarafin fitar da littafi kaɗan daidai da buƙatar marubuci, kama daga 10 ko 20 har sama da haka. Don haka idan na yi aikin nakan tallata shi a kafar yanar gizo, da sauran wurare, kuma cikin ikon Allah, masu karatu sukan tuntuɓe ni su siya na aika musu da littafin a duk wajen da suke.

Wannan hanyar bata son gaggawa, don haka idan na yi aikin littafi ba na damuwa, lallai sai yanzu-yanzu ya ƙare, zan yi haƙuri in jira har ranar da Allah zai kawo masu saya. Wani lokacin kuma nakan ɗauki kwafi na bayar kyauta na sake wani aikin.

A yanzu burina ya fi karkata in buga littafi don a karanta ba wai don abinda zan samu ba. Idan kuɗi ne mun samu a baya mun godewa Allah. Bana fatan dukkan mu a ce mun gudu mun bar adabin ya mutu. Ko na yi niyyar komawa wata sana’ar da zarar na samu kuɗi sai na ji ba zan tava iya wata sana’a idan ba rubutu ba. Don haka na sha saka kuɗaɗena na buga aiki daga nawa har na wasu.

Ganin adabin na ƙoƙarin durƙushewa na yi wa kaina wani fata na ƙoƙarin riƙe wasu littattafan marubuta ta hanyar sake dawo da su kasuwa. Duk da ba wani ƙarfi gareni ba amma haka na soma yin wannan aikin ta hanyar siyan Haƙƙin Mallaka na wani tsohon littafi daga marubucin na asali, don na sake bugawa, kamar yadda ake yi yanzu na kai kasuwa. Fatana dai kar a ce gabaɗaya adabin ya mutu.

Yaya ka ke kallon kasuwar bayan fage ta manhajojin onlayin da ake hulɗa da su a yanzu, da wancan tsohon tsarin da ku ka fi sabawa da shi na kasuwa?

Zamani idan ya zo kawai ka bi shi. Ba ka ji an ce idan ka je gari ka ga kowa da jela kai ma ka nemi tsumma ka ɗaura ba.

Wasu na ganin akwai daga cikin sabbin marubuta da ke vata sunan marubuta da harkar rubutu, don haka akwai buƙatar tsofaffin marubuta su dawo cikin harkar a gyara tafiyar, ka yarda akwai irin hakan?

Haka ne akwai sababbin marubuta da ke ɓata harkar rubutu sosai, haka nan kuma akwai masu ƙwazo da fikira. Akwai marubuta na batsa wanda baka so a ce wannan Hausawa ne suka yi rubutun ba. Mu a baya idan muka je taron wata-wata na ƙungiyar marubuta idan aka saka littafinka to, da zarar an samu batsa a ciki, wankin babban bargo za a yi maka ta yadda gobe ba za ka ƙara ba. Amma yanzu rubutu ake daga buhu sai tukunya. Wani lokacin ko gyara ka yi wa marubuciya sai ta so farfaɗa maka maganganu marasa daɗi.

Don haka su tsofaffin marubuta a sanin da na musu suna maraba da kowa haka nan kowa na su ne.

Menene gwamnati da ƙungiyoyin marubuta za su iya yi su dawo da kwarjinin harkar rubuce-rubucen adabi?

Su riƙa saka gasa a tsakanin marubuta akai-akai, hakan zai taimaka a samar da rubutu masu kyawu sosai.

Menene ra’ayinka kan tunanin marubuta su daina tsayawa kan rubutun faɗakarwa da nishaɗi kawai, su riqa duba ɓangarorin samar da littattafan tarihi ko na koyarwa a makarantu?

Hakan yana da kyau tunda shi daman marubuci yana iya leƙawa kowanne irin fage. Shi ya sa ake ce masa kamar ɗan mazari, don ko’ina kaɗawa yake yi.

Akwai ƙoƙari da wasu marubuta ke yi na ganin an samar da wata gidauniya ta bai-ɗaya domin tallafawa iyalin marubuta da suka kwanta dama, shin kana ganin cancantar yin hakan?

Hakan abu ne mai kyau sosai.

Yaya ka ke kallon zumunci da haɗin kan da marubuta ke da shi, da kuma ƙalubalen da ya kamata a gyara?

Tabbas marubuta suna da zumunci da son junansu. Allah Ya sanya albarka a wannan fannin sosai.

Idan sabon shugaban Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano ya nemi shawararka kan yadda za a inganta harkokin marubuta a Kano, me za ka ce masa?

Zan bada shawara akan ya kafa kwamiti wanda ya shafi marubuta, tunda mai ɗaki shi ya san inda yake masa yoyo. Su wannan kwamitin sun san ciwon da ke damun marubuta na rashin wadatacciyar kasuwar zamani ta sayar da littafi. Wannan kwamitin sun san duk hanyar da za su bi domin zaƙulo baragurbin marubuta. Haka nan wannan kwamitin suna da fikira na samarwa da marubuta walwala da jin daɗi.

Duk da qin shiga harkokin siyasa da marubuta suka yi a baya, amma tunda kiɗa ya sauya dole rawa ta sauya. Don haka a cikin manyan shawarwarin da zan ba shi har da duba hanyoyin da gwamnati za ta farfaɗo da harka ta hanyar ba su dama a saka wasu littattafansu a cikin makarantu duba da akwai littattafai da dama da karansu ya kai tsaiko, don haka ko’ina za a iya saka su ba tare da an ji kunya ba.

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarka?

Ƙashin cikin turmi, ba na wadan kare ba ne.

Na gode.

Ni ne da godiya.