Matashiyar da aka taɓa zargi da safarar miyagun ƙwayoyi zuwa Saudiyya ta kammala makarantar NDLEA

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Zainab Habibu Kila, wacce hukumomin Saudiyya suka zarga da safarar ƙwayoyi a shekarar 2018, a ranar Juma’ar da ta gabata ta kammala karatunta a makarantar horar da dabarun kama miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) da ke Jos.

Mahaifinta, Habibu Kila ya raba hotunan bikin yaye ɗaliban yayin da yake godiya ga Allah.

An tuhumi Zainab Kila bisa kuskure da laifin safarar miyagun ƙwayoyi zuwa ƙasar Saudiyya a shekarar 2018, kuma an tsare ta na kwanaki kafin gwamnatin Nijeriya ta shiga tsakani aka sake ta.

Wata ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi ce ta tsara matar ’yar Jigawa yayin da ta je aikin Hajji a ƙasar Saudiyya a shekarar 2018 ta filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da ke MAKIA, tare da mahaifiyarta Maryam da kuma ’yar uwarta Hajara.

A ranar 26 ga watan Disamba, 2018 ne hukumomin ƙasar Saudiyya suka kama ɗalibar a Jami’ar Maitama Sule da ke Kano bisa zargin tafiya da jakunkuna ɗauke da wasu haramtattun abubuwa da ake kyautata zaton tramadol ne.

A filin jirgin sama na Jeddah, Hukumomin Saudiyya sun damƙe jakar, inda daga bisani suka gano Zainab tare da kamata a ɗakinta na otal.

Hukumar yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasar Saudiyya ta tuhume ta tare da tsare ta tsawon watanni huɗu bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi.

Bayan wasu kiraye-kirayen da iyayenta da kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyin farar hula suka yi, hukumomi sun gano cewa ɓarayin miyagun ƙwayoyi tare da haɗin gwiwar ma’aikatan filin jirgin saman Kano sun sanya wa wata jaka ɗauke da ƙwayoyi da sunan ta.

An sake ta ne bayan hukumomin Nijeriya da na Saudiyya sun gudanar da bincike kan lamarin tare da tabbatar da cewa ba ta da wani laifi. An saki Zainab a ranar 30 ga Afrilu, 2019 kuma ta dawo gida bayan makonni biyu.

Zainab Habibu Kila na cikin sabbin jami’an NDLEA 2,000 da aka horar a makarantar horas da hukumar da ke Jos, jihar Filato a ranar Juma’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *