Daga BELLO A. BABAJI
Matatar Ɗangote ta sanar da ɗaga farashin fetur ga kwastomominta, wata guda bayan rage farashin da ta yi a lokacin bukukuwan ƙarshen shekara.
A ranar Juma’a ne ta ce ta mayar da farashin litar mai N955 daga wajen dakonsa wanda hakan ya nuna an samu sauyi game da farashin.
Ƴan kasuwar da ke sayan lita miliyan 2 zuwa 4.99, za su riƙa sayen kowacce lita a N955, yayin da masu sayan lita miliyan 5 zuwa abin da ya yi sama za su riƙa biyan N950 a duk lita.
Hakan ya nuna cewa an samu karin N55.5 akan N899.50 da aka saba sayarwa daga watan Disambar shekarar da ta gabata.
Sanarwar ta ƙara da cewa karin zai fara aiki ne daga ƙarfe 5:30 na yammacin ranar 17 ga watan Junairu, 2025.