Daga ALI MUHAMMAD
Bayan shekaru 4 da aka shafe ana gurzuwa cikin masifa mara adaɗi, a lokacin da Matawalle yake ayyuka kamar na ‘yan ta’adda marasa imani ko ‘yan fashi a gefen filin Sahara, yana varnatar da dukiyar jihar Zamfara yayin da jihar take qara kasancewa abar tausayi kuma maƙasƙanciya, bai kamata a ce an yi wa Matawale sakayyar mugun mulkinsa da kujerar minista ba.
Matawalle ya yi iƙirarin an kashe kimanin Naira biliyan 3 a kan tsaro da sayen kayan aikin kyamarar tsaro.
Mecece alaƙar Matawalle da kamfanin haɗa magungunana ’’dot.com‘’ wanda aka ba wa kwangilar Naira biliyan guda don samar da ababben hawa?
Bello Matawalle wani mutum ne da ya zama Gwamna bisa tsautsayi a shekarar 2019 zuwa 2023 wanda ba za a taɓa mantawa da shi ba saboda tsunduma jihar Zamfara da ya yi cikin haɗarurrukan shiga talauci da matsin tattalin arziki masu dogon zango.
Mutanen Zamfara ba su tava zaɓensa ba, kawai dai ya rabauta ne da hukuncin Shari’a wanda ya yi watsi da fatali da dukkan ‘yan takarar APC da suka lashe zaɓe (tun daga kan gwamna har zuwa ‘yan majalisar jiha da suka yi nasara) saboda laifin rashin gudanar da zaven fidda gwani na cikin jamiyya. Kasancewarsa wanda ya zo na biyu a a zaɓen gwamna, Matawalle ya samu damar shigewa gidan gwamnatin jihar.
Sam ba abin mammaki ba ne don buqatar Matawale ta sake zarcewa a zangon mulki na biyu a 2023, ta gamu da tazgaro kuma ta faɗi wanwar. Domin kuwa, rahotanni sun nuna cewa, an sanya shi a jerin gwamnoni marasa tsinana wa yankunansu komai a tarihi. Wato daga shekarar 2019 zuwa 2023 bisa rahoton bincike.
Shekarun da aka shafe a ƙarƙashin mulkin Bello Matawale, sun yi ƙaurin suna a matsayin shekarun da suka zamo asara a rayuwar mutanen jihar Zamfara.
Wani sahihin rahoton bincike mai inganci a kan lokacin mulkin Matawalle ya bayyana cewa, da matuƙar wuya ko ma ba zai yiwu a ɗaga wasu ayyuka waɗanda za su amfani al’umma a nuna wanda aka yi a lokacin mulkinsa ba.
Albashin ma’aikatan jiha an riƙe shi tsahon watanni, ya zama bashi. Wasu lokutan ma ba a biya sam, asibitocin sun kasance cikin halin ha-ula’i, waɗanda gwamnatin jiha take kula da su kuma sun zama sai du’a’i, shi kuwa da ma ilimin firamare da na sakandare ko zancensu ma ba a yi.
Amma kuma, dukka waɗannan ayyukan da kuma ma’aikatun duk akwai wani kason kuɗaɗe da ake ware musu a cikin kasafin kowacce shekara waɗanda suke yin vatan dabo a cikin aljihun Gwamnan.
Ya kamata a tuna cewa, a ƙarƙashin gwamnatin Matawale ne, rashin tsaro da harkar daba ta zama tambarin jihar zamfara.
Akwai matsalolin vacewar ‘yan jihar, wato waxanda suka gudu daga ƙauyukansu saboda addabar ‘yan daba da ɓarayin shanu. Kai ka ce su ma ɓata garin suna rigegeniya da gwamnan wajen figewa da kwashe dukiyar al’ummar jihar Zamfara.
Ya kamata a nemi Matawalle ya bayyana a kafafen yaɗa labaran Nijeriya domin yin sahihiyar tattaunawa da shi don bayyana wai shin nawa ya kashe wajen ‘yin sulhu’ da yake ikirarin ya sha yi da ‘yan daba a tsahon wa’adinsa a kan kujerar mulki. Maganar gaskiya bai kamata a ce an kashe waɗannan maƙudan kuɗaɗe ba wajen yin sulhun da sam ba a ga sakamakonsa a ƙasa ba.
Akwai kyakkyawan zato mai qarfi cewa, tsohon Gwamnan wai har ya samu ƙarfin halin cewa ya kashe kimanin Naira biliyan 3 a samar da kyamarar tsaro da sauran na’urorin tsaro da suke da alaƙa da su. Amma wannan bai hana al’ummar Zamfara cigaba da fuskantar azabar rashin tsaro ba.
Akwai ranar qin dillanci wacce za ta tilasta dole Matawalle ya tsage gaskiyar inda ya adana kayan tsaro na kimanin Naira Miliyan 700, idan ma ya sayi kayan kenan. Shin akwai wata riba da ko sakamako da mutanen jihar suka rabauta daga wannan kyamarar tsaro?
Abinda hankali ba zai ɗauka ba ne a ce a jihar da talauci ya yi mata ɗaurin gwarmai kuma Gwamna Matawalle zai ɓarnatar da kusan Naira biliyan biyu don biyan harajin kwastam, shatar jirgin ruwa, sufuri da sauran kashe-kashen kuɗaɗe masu alaƙa da wannan a lokacin mulkinsa. Waɗannan buƙatu su ne a kansu tsohon jagoran hukumar zartarwa ta jihar Zamfara ya ɓatar da kuɗaɗen al’umma.
Zangon mulkinsa shi ne asalin yadda ake yi wa tattalin arzikin Afirka ƙamshin mutuwa, Matawalle ya gurɓata dukkan wata hanya ta samar da cigaba a jihar a tsahon shekaru 4 da ya gudanar da kasasshiyar gwamnatinsa.
Akwai wani bincike da kwamitin ‘yan jarida masu kishin al’umma suke kan gudanarwa tare da gamayyar al’umma da suke bibiyar badaqala da muna-muna da Gwamna Matawale ya yi a harkar kuɗi a jihar Zamfara da kuma tarin kafanonin da suka taimaka masa wajen mummunar satar da ya yi wa al’ummar jihar Zamfara.
Misali, meye alaƙar Gwamnan da kamfanin haɗa magunguna na dot.com da aka bai wa kwangilar Naira biliyan 1 don samar da ababen hawa?
Aƙidar sabunda tsammani, wadda take shimfiɗa hanyar gwaggwavan cigaba da manufar cewa ‘yan ƙasa za su ƙara ba da gudunmowa don samar da sabuwar Nijeriya, bai kamata a ce wannna aqida ta ba da gurbi ga ire-iren su Matawale ba su shiga fadar shugabancin qasa.
Abinda kawai zai ƙara ƙarfafa gwiwa da zai isar da saƙo na kwantar da hankali ga al’ummar jihar Zamfara da gabaɗaya ‘yan Nijeriya shi ne, su ga tsohon gwamnan na jihar Zamfara ya gurfana gaban Shari’a don a tabbatar da laifinsa ko akasin haka.
Hakazalika, a girmama mutum kamar Matawale da muƙami a fadar shugaban ƙasa wani abin takaici ne, kuma gingimemen kuskure ne ga gwamnati.