Matawalle ya buɗe Gasar Karatun Alƙur’ani ta Ƙasa karo na 37

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau

A ranar Juma’a Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya ƙaddamar da Gasar Karatun Alƙur’ani mai tsarki ta ƙasa karo na 37 da gwamnatinsa ta ɗauki nauyin gudanarwa a Gusau babban birnin jihar.

Da yake ƙaddamar da gasar, Gwamna Matawalle ya bayyana gasar a matsayin wani nau’i na haɗin kan Musulmi a ƙasar nan.

Ya ce, gasar za ta bai wa Nijeriya damar zaɓar waɗanda za su wakilci ta a Gasar Ƙur’ani ta Ƙasa da Ƙasa a tsakanin waɗanda suka fafata a gasar.

Kazalika, ya ce gasar za ta taimaka wajen gudanar da addu’o’in samun zaman lafiya ga ƙasa.

A nasa jawabin, Shugaban taron kuma Gwamnan Jihar Borno, Baba Gana Umar Zulum, ya yaba wa Gwamnatin Jihar Zamfara bisa ɗaukar nauyin gasar karo na 37.

Gwamna Zulum ya bayar da gudunmawar Naira Miliyan 10 domin tabbatar da gasar ta gudana cikin nasara.

Ya kuma buƙaci al’ummar musulmi da su yi addu’ar Allah ya dawo da dauwamammen zaman lafiya a ƙasar nan, tare da yin kira ga musulmi da a ci gaba da haɗa kai domin cigaban addinin Musulunci da karatun Alƙur’ani a Nijeriya.