Matawalle ya dawo da wasu tuɓaɓɓun kwamishinonisa, ya dakatar da sarakuna biyu

Daga WAKILINMU

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya sake naɗa wasu daga cikin kwamishinonin da ya sauke a baya da kuma naɗa wasu shugabannin hukumomin gwamnati.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar 1 ga watan Yuni, 2021, Gwamna Matawalle ya sauke Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Bala Bello tare da kwamishinoni 23.

Bayanin dawo da Kwamishinonin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da ta samu sa hannun Shugaban Ma’aikatan Jihar kuma Muƙaddashin Sakataren Gwamnatin Jihar, Kabiru Balarabe, a ran Talata a Gusau, babban birnin jihar.

Kwamishinonin da aka sake dawo da su, su ne Alhaji Ibrahim Dosara a matsayin Kwamishinan Labarai da Alhaji Sufyanu Yuguda a matsayin Kwamishinan Kuɗi da kuma Hajiya Fa’ika Ahmad a matsayin Kwamishinar Harkokin Jinƙai.

Sai kuma Abubakar Sodangi da aka naɗa a muƙamin Shugaban Hukumar Zakka da Ali Muhammad-Dama a matsayin Shugaban Hukumar Tara Kuɗin Shiga.

A hannu guda, Matawalle ya dakatar da Sarkin Dansadau, Hussaini Umar da Dakacin Nasarawa Mailayi, Bello Wakkala nan take tare da ba da umarnin a binciki harkokin sarakunan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *