Matawalle ya kafa sabbin dokokin tsaro 7 don yaƙi da matsalolin tsaron Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

A matsayin wani mataki na ci gaba da yaƙi da matsalolin tsaro a Jihar Zamfara, Gwamnan Jihar, Dr. Mohammed Bello Matawalle, ya kafa wasu sabbin dokoki har guda bawkai waɗanda kuma aka buƙaci al’ummar Zamfara su kiyaye su don taimaka wa gwamnatin jihar wajen cimma ƙudurinta na neman ganin bayan matsalolin tsaro a jihar.

Cikin wata sanarwar manema labarai da Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Zamfara, CP Ayuba N. Elkanah, ya fitar a ranar Lahadi ta zayyano waɗannan dokoki da suka haɗa da: Haramta cin kasuwannin mako-mako a faɗin jihar, haramta sayar da man fetur a jarkoki, haramta zirga-zirgar babura da keke Napep a cikin birnin Gusau daga ƙarfe 8 na dare zuwa 6 na safe, sannan daga ƙarfe 6 na yamma zuwa 6 na safe a sauran yankunan ƙananan hukumomin jihar.

Sauran dokokin su ne: Haramta wa gidajen mai saida wa motocin kasuwa fetur na sama da N10,000, haramta jigilar itacen hura wuta a sassan jihar, dakatar da jigilar dabbobi zuwa wajen jihar, da kuma binciken ƙwa-ƙwaf ga masu shigo da dabbobi jihar daga waje, sai kuma haramta wa babura ɗaukar mutum fiye da biyu a lokaci guda.

Da yake jawabi ga manema labarai, kwamishinan ya ce Gwamna Matawalle ya shata waɗannan dokin ne a Juma’ar da ta gabata bayan da ya tuntuɓi hukumomin tsaron jihar da sauran masu faɗa a ji a jihar.

Da wannan ne Kwamishinan ya ce, “Ina amfani da wannan dama wajen sanar da al’ummar Zamfara cewa, rundunar ‘yan sanda da takwarorinta a jihar a shirye suke wajen tabbatar da cewa ‘yan jihar sun kiyaye waɗannan dokoki.

“Daga gobe Litinin, za mu kafa runduna ta musamman wadda za ta riƙa zagayawa sassan jihar don tabbatar da ba a yi wa waɗannan dokoki karan tsaye ba.”

Kwamishinan ya ƙara da cewa, jami’an tsaron jihar ba su ɗauki aikinsu da wasa ba, don haka ba za su rangwanta wa duk wanda aka kama da laifin ƙin yin biyayya ga waɗannan sabbin dokokin ba.

Daga nan, ya buƙaci ‘yan jihar da kowa ya ba da tasa gudunmawa wajen ci gaba da yaƙi da matsalolin tsaro da ake yi a jihar. Tare da bai wa ‘yan jihar shawarar su zamo masu bin doka da oda a kowane lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *