Matawalle ya rufe tashoshin yaɗa labarai huɗu bisa zargin yaɗa taron PDP

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Gwanatin Jihar Zamfara ta bada umarnin gaggawa na rufe tashoshin yaɗa labarai guda huɗu da ke Gusau, babban birnin jihar.

Jawabin rufe tashoshin ya fito ne daga bakin kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Ibrahim Dosara, a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai ranar Asabar.

Dosara ya bayyana cewar tashoshin da lamarin ya shafa sun haɗa da Tashar Talabijin ta NTA da Radio Pride FM da Al’umma TV da kuma Tashar Talabijin ta Gamji TV.

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa, rufewar ya biyo bayan wani rikicin siyasa da ya yi sanadin mutuwar wasu mutum uku da raunata da dama da ya auku a tsakanin magoya bayan Jamiyyar PDP da na APC ranar Asabar da ta gabata a Gusau jim kaɗan bayan da ɗan takarar gwamnan jihar na PDP, Dr. Dauda Lawal Dare ya shigo garin Gusau.

Sai dai jaridar Intelregion ta rawaito cewa, Gwamna Bello Matawalle ya ba da umarnin rufe tashoshin ne bisa zargin ɗauka da yaɗa harkokin taron ɗan takarar gwamna na PDP a jihar, Dauda Lawak, da ya gudana ranar Asabar a jihar.

Kazalika, jaridar ta ce gwamnatin jihar ta bai wa Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Yusuf Kolo, umarnin kama dukkan ‘yan jaridar da suka halarci taron.

Majiyarmu ta ce duk da dai Dosara bai bayyana dalilan da suka sanyan gwamnatin jihar ɗaukar matakin rufe kafafen ba, amma ana kyautata zaton haka ba zai rasa nasaba da yaɗa harkokin taron kai-tsaye da kafofin suka yi ba

Da yake mayar da martani a zantawarsu da BBC Hausa, tsohon Ministan Yaɗa labarai, Alh. Ikea Aliyu Bilbis, ya bayyana cewa babu wata gwamnatin jiha da ke da ikon rufe kafofin yaɗa labarai mallakar Gwamnatin Tarayya ba tare da izinin gwamnatin ba.

Hakazalika, shugaban gidan radiyon Pride FM mallakar Radio Nigeria Kaduna, Malam Mujitaba Ramalan Bello, ya jaddada cewar za su ci gaba da aiki bisa doka ba tare da nuna wani bambancin siyasa ko ra’ayi ba.

Manhaja ta kalato cewar, biyu daga cikin kafafen da lamarin ya shafa mallakar gwamnati ne, wato NTA da Pride FM, sannan biyun da suka rage masu zaman kansu ne, wato Tashar Gamji da Al’umma FM.