Matawalle ya sanya wa dokar cin gashin kai na ɓangaren sharia da Majalisar Dokoki hannu

Daga SANUSI MUHAMMAD, a GUSAU

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya ba da damar aiwatar da ƙudirin dokar cin gashin kai ga ɓangaren shari’a da majalisar dokokin jihar Zamfara.

Babban Daraktan Wayar da Kan Jama’a da Sadarwa, Yusuf Idris, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Gusau ranar Alhamis.

A cewarsa, Gwamnan ya rattaba hannu kan dokokin ne a wani takaitaccen biki wanda aka gudanar a Fadar Gamnatin jihar da ke Gusau, biyo bayan mahimmancin da gwamnan ya bai wa dokokin biyu, ya ce ba zai jira wani babban biki da za a shirya ba don sanya hannu kan yarjejeniyar dokar.

Ya ce, “Sabbin dokokin biyu yanzu su ne Dokar ‘Yancin Yankin Shari’a ta Jihar Zamfara da Dokar Gudanar da Majalisar Dokokin Jihar Zamfara da Abubuwan da ke da Alaƙa da hakan, 2021 (1442 AH).”

Yayin sanya hannu a kan ƙudirin zuwa doka, Matawalle ya nuna cewa a matsayinsa na mai ƙoƙarin tabbatar da ɗorewar dimokiraɗiyya ta gaskiya, zai ci gaba da tabbatar da cewa dukkanin ayyukan da doka ta sanya su an karkata su zuwa hanyoyin da suka dace.

Yana mai cewa, “Ban ga wani dalili da zai sa mu ba da damar cin gashin kan waɗannan ƙarfi da ƙarfi na gwamnatin ba wanda zai tabbatar da tafiyar da gwamnati cikin sauƙi da cigaban jiharmu.

“Ba za mu sanya siyasa ko wasa da nauyin da ke wuyanku ba, kuɗaɗenku da kuma cin gashin kanku, saboda haka, da wannan sanya hannu a kan doka, ina da ƙwarin gwiwa cewa za mu ci gaba da aiki a matsayin ƙawayenmu don cigaban jiharmu da al’ummarta.”

Ya kuma yi kira gare su da su kiyaye duk wani fasadi kana ya umarce su da su kawar da duk wanda aka samu yana son aikata hakan.

Da yake maida martani, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Rt. Hon. Nasiru Ma’azu Magarya, ya yaba wa gwamnan kan yadda ya ƙulla kyakkyawar alaƙa da Majalisar Dokoki da kuma ɓangaren shari’a na jihar, wanda hakan ya sa ɓangarorin gwamnati uku suka zama cikakkun ‘yan’uwa masu riƙon amana.